Harin Borno: Tabbas Ƴan Ta’adda Za Su Fuskanci Hukunci — Shettima


Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sha alwashin cewa waɗanda suka kai harin bam a wani masallaci da ke Kasuwar Gamboru a Maiduguri, Jihar Borno, ba za su tsira ba, inda ya ce za su fuskanci cikakken hukuncin doka. Harin da ya faru a daren Kirsimeti ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.

Shettima ya yi kakkausar suka ga harin, yana mai bayyana shi a matsayin mummunan ta’addanci da aka aikata kan fararen hula marasa laifi da zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya. Ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara tsaro a Jihar Borno domin kamo masu hannu a harin.

  • Borno Da Kano Sun Zama Zakaru A Gasar Karatun Alƙur’ani Ta Ƙasa Ta 2025
  • Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya na tura ƙarin rundunonin tsaro na musamman zuwa yankin domin farautar ƴan ta’addan da kuma gurfanar da su gaban shari’a. Ya jaddada cewa ba za a amince da duk wani yunƙuri na tayar da zaune tsaye ba.

Gwamnatin Tarayya ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron ƙasarmu ba. Hukumomin tsaro suna aiki dare da rana domin tabbatar da cewa an kama tare da hukunta masu aikata wannan mummunan laifi,” in ji Shettima. Ya kuma nuna tabbacin cewa tsarin tsaron da ake da shi zai fallasa dukkanin bayanan da suka shafi harin.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Borno, da al’ummar Maiduguri da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta ja da baya ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ƴan Nijeriya ba.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *