Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka
[ad_1]
Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu laifukan da suka haɗa da kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu.
Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin kashe mijinta, ba ta cikin sabon jerin sunayen wadanda aka yafe wa laifi. Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunayen mutane kimanin 50 daga tsohon jerin bayan ce-ce-ku-ce daga jama’a.
“Bayan duba martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane daga jerin wadanda aka bai wa afuwa,” in ji Onanuga.
Ya kara da cewa an dauki wannan mataki ne “don mutunta ra’ayoyin jama’a, karfafa gwiwar jami’an tsaro, da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da al’umma baki daya.”
Tsohon jerin sunayen da aka fitar ya haifar da suka daga jam’iyyun adawa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, wadanda suka bayyana matakin a matsayin amfani da ikon shugaban kasa ta hanyar da bata dace ba, kuma barazana ga tsarin shari’a. Sun yi gargadin cewa sakin manyan laifuka zai iya karfafa aikata laifi da kuma rage amincewa da doka.
Fadar shugaban kasa ta ce sabon umarnin yana nufin tabbatar da gaskiya da amincewa a tsarin bayar da afuwa. Shugaba Tinubu ya kuma umarci a dora aikin bayar da afuwa a karkashin ma’aikatar shari’a, tare da shigar da hukumomin tsaro da na shari’a a cikin tsarin don kauce wa irin wannan ce-ce-ku-ce a gaba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link