Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC




Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa jiragenta da ke jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna, za su koma aiki a mako mai zuwa.

Mai magana da yawun NRC, Callistus Unyimadu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Asabar, duk da yake bai sanar da haƙiƙanin ranar da za a koma aikin ba.

Callistus, ya ƙara da cewa matakin ya biyo bayan nasarar kammala gyare-gyare da bincike a ɓangaren da aka samu matsala a baya-bayan nan.

A cewarsa, hukumar na yin aiki ba tare da gajiyawa ba don tabbatar da cewa an samar da kayayyakin aiki na zamani waɗanda za su yi gogayya da na sauran ƙasashen duniya.

Tun a ranar 26 ga watan Agustan da gabata ne NRC ta dakatar da sufurin jirgin ƙasan da ke jigila a tsakanin Abuja zuwa Kaduna bayan tuntsurewar da ya yi yana tafe da fasinjoji.

Shugaban NRC Kayode Opeifa, ya sanar da cewa hukumar ta ɗauki wannan matakin ne har sai an kammala bincike kan hatsarin jirgin da ya auku.

Opeifa ya yi watsi da maganganun da ake yi cewa jiragen ba su da inganci, yana mai cewa an fara mayar da kuɗin tikiti ga dukkan fasinjojin da abin ya shafa.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *