Sabbin Hare-haren Ta’addanci: Ba Za Mu Yarda Matsalar Tsaro Ta Dakushe Kokarinmu Na Bunkasa Kasa Ba –Tinubu
[ad_1]
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi ikirarin cewa; gwamnatinsa za ta kara zage damtse, wajen tunkarar kalubalen rashin tsaro a fadin kasar nan, inda ya bayar da tabbacin kare lafiyar ‘yan kasar a tarukan da aka gudanar a Kasar Birtaniya.
Tinubu, wanda ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da gwamnoni 23 a gidansa da ke Legas, domin gudanar da bukukuwan Sallah Karama ya ce, ya bi diddigi tare kuma da goyon bayan matakan tsaro na zamani tare da Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron.
- Trump Ya Yi Barazanar Kwace Man Iran Yayin Da Rikici Ke Sake Ruruwa
- CMG Ya Yi Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Lokacin Bazara” A Hadaddiyar Daular Larabawa
Kasancewarku a nan a yau, yana nuna gaskiya, sadaukarwa da kuma darajar da kuke da ita wajen aiwatar da hadin kai.
“Babban abin da muke fuskanta, yake kuma ci mana tuwo a kwarya a halin yanzu shi ne, batun kalubalen rashin tsaro a kasar.
“Ina yin dukkan kokarin da ya dace, domin ganin mun samu nasara a kan wannan ta’addanci da rashin tsaro da muke fama da shi.
“Kazalika, na himmatu wajen karfafa abokan hulda da hanyoyin sadarwa, wadanda suka zama dole, sannan daya daga cikin manyan abubuwan da muka tattaunawa a Burtaniya, sun hada da samar da kayan aiki da kuma tallafi.
“Zan kuma iya yi muku albishir na cewa, a jiya na yi doguwar tattaunawa da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a kan batun samar da kayan aiki da kuma tallafi. Ina kuma ci gaba da yunkurin tuntubar wasu kasashen,” in ji shi.
A ranar Juma’a ne, shugaba Tinubu da uwargidansa, Oluremi Tinubu, suka dawo daga ziyarar aiki ta kwanaki uku da suka kai Kasar Birtaniya, inda Sarki Charles III da Sarauniya Camila suka karbe su.
Shugaban ya kuma yi wata ganawa da Firaministan Kasar Birtaniya, Keir Starmer, kafin ya dawo Nijeriya, domin gudanar da bikin sallah karama.
“Ya kamata mu kara kula da masu rauni. Dalili kuwa, na san wannan rikicin na Gabas ta Tsakiya, zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki. Haka zalika, kungiyar kwadago da sauran wasu kungiyoyi, za su yi shiri domin neman karin tallafi, sakamakon wannan rikici na Gabas ta Tsakiya, “in ji shugaban.
Har ila yau, shugaban ya kuma bukaci gwamnonin jihohin, su dage tare da juriya wajen aiwatar da tsare-tsaren da suka dace, domin sama wa ‘yan kasa sauki kai tsaye, tare da mara wa gwamnati baya wajen tinkarar “zalunci” na masu aikata laifuka.
Shugaba Tinubu ya shawarci gwamnonin da su kara bayar da kwarin guiwa, domin dakile illar hauhawar farashin kayayyaki, sakamakon wannan yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Haka zalika, ya mika godiyarsa ga mataimakin shugaban kasa, Sanata. Kashim Shettima, bisa ziyarar jaje da ya kai Jihar Borno, inda ya bai wa jama’ar jihar tabbacin samun karin kariya ta hanyar fasahar zamani.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya, kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, ya gode wa shugaban kasar, kan tsoma bakin da ya yi a jihohin tare da aiwatar da ajandar shirin nan na ‘Renewed Hope’.
A madadin takwarorina, gwamnoni, muna miko gaisuwa tare da yi maka barka da sallah, muna kuma godiya ga Allah Madaukakin Sarki, da ya nuna mana karshen watan Ramadan lafiya.”
Haka zaliika, shugaban ya taya shugaban kasar murnar nasarar da ya samu ta ziyarar aiki da ya kai Kasar Birtaniya da kuma yarjejeniyar zuba jari da aka cimma.
“Babbar manufarmu ita ce, kulla kyakkyawar alaka da Burtaniya, ziyarar kasar ta farko a cikin shekara 37 na da matukar muhimmanci tare da kulla sabuwar alaka da Nijeriya, muna matukar godiya.
“Dole ne mu tabbatar da cewa, batun rashin tsaro ya zo karshe, sannan batun ‘yansandan jihohi, ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro daban-daban a karkashin jagorancin mai bayar da shawara a kan harkokin tsaro, kungiyar gwamnoni kuma tana ba da gudunmawar da ta dace domin tabbatar da al’amarin, kazalika kungiyar za ta kai takardar zuwa Majalisar Dokoki ta Kasa, domin ganin yadda za mu iya samun tsarin doka ga ‘yansandan jihohin,” in ji gwamnan.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da: Sanata Hope Uzodinma, Jihar Imo; Aled Otti, Jihar Abia; Umo Eno, Jihar Akwa Ibom; Douye Diri, Jihar Bayelsa; Hyacinth Alia, Jihar Benue; Bassey Otu, Jihar Kuros Riba; Sheriff Oborebwori, Jihar Delta; Francis Nwifuru, Jihar Ebonyi; Monday Okpebolo, Jihar Edo; Peter Mbah, Jihar Enugu; Mohammed Inuwa Yahaya, Jihar Gombe; da Umar Namadi, Jihar Jigawa.
Sauran kuma sun hada da: Abba Kabir Yusuf, Jihar Kano; Dikko Umaru Radda, Jihar Katsina; Ahmed Usman Ododo, Jihar Kogi; Babajide Sanwo-Olu, Jihar Legas; Abdullahi Sule, Jihar Nasarawa; Caleb Mufwang, Jihar Filato; Siminalayi Fubara, Jihar Ribas; Agbu Keffas, Jihar Taraba; Mai Mala Buni na Jihar Yobe da Lucky Aiyedatiwa, Jihar Ondo.
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, shi ma ya halarci taron.
[ad_2]
Source link