SDP Ta Gargadi INEC Kan Yin Katsalandan A Harkokin Jam’iyyar
[ad_1]
Jam’iyyar SDP ta gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan yin katsalandan a cikin harkokinta, tana mai jaddada cewa jam’iyyar ce kawai za ta iya yanke hukunci kan harkokinta na cikin gida.
Jam’iyyar ta yi maraba da hukuncin kotun koli da ta ki amincewa da shari’ar da INEC ta shigar kan rikicin shugabancinta, inda ta bayyana wannan hukunci a matsayin babban nasara ga dimokuradiyya da ‘yancin jam’iyya da kuma bin dokar kasa.
- Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami
- An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 15 Da Kafuwar Asibitin Abota Na Sin Da Ghana
A cikin hukuncin da ta yanke a ranar Jumma’a, kotun koli ta ki amincewa da korafin INEC na kalubalantar shugabancin SDP kuma ta umarci biyan naira miliyan 2 a matsayin kudin tara ga hukumar. Kotun koli ta bayyana korafin a matsayin wanda bai dace ba kuma ya saba wa doka.
INEC ta nemi a soke hukuncin 17 ga Oktoba na kotun daukaka kara da ke Abuja, wanda ya tabbatar da hukuncin babban kotun tarayya wanda ya tilasta wa hukumar ta amince da kuma hada ‘yan takarar SDP a zabukan cike gurbi a jihohi 12.
A yayin da yake magana a taron manema labarai a shalkwatar jam’iyya da ke Abuja bayan yanke hukuncin, mukaddashin shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Sadik Gombe, ya ce hukuncin kotun kolin ya tabbatar da matsayin shari’a da aka dade ana yi da cewa harkokin cikin gida na jam’iyyu bai kamata a samu tsoma baki daga waje ba.
“Wannan hukuncin yana da matukar muhimmanci, ba wai ga SDP kadai ba, har ma ga dukkan jam’iyyun siyasa a Nijeriya. Yana tabbatar da matsayin kotun koli na cewa al’amuran cikin gida na jam’iyyun siyasa, jam’iyyun ne kadai za su yanke hukunci a kai,” in ji shi.
Gombe ya bukaci INEC ta cika hukuncin gaba daya ta hanyar ba wa jam’iyyun siyasa damar gudanar da harkokinsu na ciki bisa tsarin kundinsu. Har ila yau, ya yi kira ga jam’iyyun da su kiyaye dabi’a na ciki gida da bin tsarin da ya dace.
“Muna godiya wa bangaren shari’a. Muna fatan wannan hukunci zai kara karfafa dimokuradiyyarmu da dokar kasa yayin da muke tukarar zaben 2027. Mun fahimci damuwarsu da sha’awarsu, duk da haka adalci dole ne ko da yaushe ya yi rinjayi. Muna sa ran INEC daga yanzu za ta daina tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa, domin wannan batun tun da farko kotun koli ta yanke hukunci tare da warware zare da abawa. Hukumar kuma dole ta daina duk wani mu’amala da mambobi da aka dakatar ko aka kore daga jam’iyya kuma ta amince nan take da sauya shugabancin mukaddashin jam’iyyar na kasa Shehu Gabam,” in ji shi.
A yayin mayar da martani ga hukuncin, babban lauya na SDP kuma dan takarar jam’iyyar na shugaban kasa a 2023, Adewole Adebayo, ya ce hukuncin ya aika da gargadi a fili ga INEC da ta guji ayyukan da za su iya raunana dimokuradiyyar jam’iyyun siyasa da dama a Nijeriya.
“Na bayyana wa INEC cewa su daina tsoma baki a harkokin ciki na SDP da sauran jam’iyyun siyasa. Dimokiradiyyar jam’iyyun da dama na bukatar alkalin da ba ya nuna bambanci ba, ba wanda ke haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyun adawa,” in ji Adebayo.
Adebayo ya bayyana cewa rikicin ya taso ne bayan jam’iyyar ta nada shugaban jam’iyyar na kasa na wucin gadi wanda ta rubuta wa INEC don tatace ‘yan takara, inda hukumar ta ki amincewa da shi, ta zabi ma ta yi mu’amala da shugaban da jam’iyyar ta riga ta kora.
Jam’iyyar ta tabbatar da cewa hukuncin kotun koli ya kara karfafa mata kwarin gwiwa tare da una cewa kotu ba ta yarda da tsoma baki daga hukumomin tsara dokoki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa ba.
[ad_2]
Source link