2027: Tsohon Ministan Buhari zai yi takarar shugaban ƙasa a ADC

[ad_1]



Tsohon Ƙaramin Ministan Ilimi a zamanin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Emeka Nwajiuba, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Nwajiuba, wanda ya taɓa wakiltar mazabarsa tsawon wa’adi biyu a Majalisar Wakilai, ya ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu na buƙatar shugabancin mai hangen nesa, wanda zai iya tsara ingantattun manufofi, gudanar da tattaunawa mai tasiri da kuma ƙarfafa siyasar tushe.

A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar Litinin, tsohon ministan ya ce gogewarsa a Majalisar Dokoki, ɓangaren zartarwa da kuma muhimman hukumomin ƙasa ya ba shi cikakken fahimta kan harkokin mulki, kuɗaɗen gwamnati da tsara manufofi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Nwajiuba zai assasa tubalin yaƙin neman zaɓensa ne kan inganta harkar ilimi, daidaita tattalin arziki da kuma dawo da amincewar jama’a kan hukumomin gwamnati, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan ci gaban ƙasa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ƙwarewa, zurfin tunanin manufofi da sanin yadda hukumomi ke aiki za su kasance manyan tubalan shugabancin da yake shirin bayarwa.

“Da wannan bayyana aniya, Nwajiuba ya shiga jerin ’yan siyasar da ke shirin taka rawa wajen tsara tattaunawar ƙasa gabanin babban zaɓe mai zuwa, yayin da muhawara kan cancanta, ƙwarewa da shugabanci mai haɗa kai ke ƙara ƙarfi,” in ji sanarwar.

Tsohon ministan ya taɓa neman takarar shugabancin ƙasa a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, amma bai samu nasarar tsallake matakin fidda gwani ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *