Sin: Bincike Mai Lamba 301 Da Amurka Ta Yi Ya Bata Tsarin Tattalin Arzikin Duniya
[ad_1]
Kwanan baya, wani kakakin ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ya amsa tambayar da dan jarida ya yi masa game da sanarwar da ofishin wakilin harkokin cinikayyar kasar Amurka ya fidda, cewar zai kaddamar da bincike mai lamba 301 kan kasashe da yankuna guda 60, ciki har da kasar Sin, bisa hujjar “Ba su daina fitar da hajojin da aka samar ta hanyar tilasta wa wasu yin aiki ba.”
Kakakin ya ce, kafin haka, kasar Amurka ta taba daukar matakan hana cinikayyar kasar Sin sau da dama, bisa karyar da ta yi game da “tilasta wa wasu yin aiki”, kasar Sin ta kuma bayyana matsayinta kan batun sau da dama, tana kuma adawa da tilasta wa wani ko wasu yin aiki a ko da yaushe, kana ta zartas da yarjejeniyoyin ’yan kwadago na duniya guda 28, tare da kafa cikakken tsari na dokar kwadago.
Har zuwa yanzu, kasar Amurka ba ta zartas da kulla yarjejeniyar hana tilasta wa wani ko wasu yin aiki ta shekarar 1930 ba, kuma ta ki bin manufofin duniya. A sai daya kuma, sau da dama ta siyasantar da batun tilasta wa wani ko wasu yin aiki. A wannan karo kuma, kasar Amurka ta kaddamar da bincike mai lamba 301 domin kafa kariyar ciniki.
A halin yanzu, kasar Sin da kasar Amurka suna gudanar da tattaunawar cinikayya ta sabon zagaye a birnin Paris na kasar Faransa, kasar Sin tana son yin shawarwari da kasar Amurka kan batun, domin sa-kaimi ga kasar don ta gyara kuskurenta. Haka kuma, kasar Sin za ta mai da hankali kan binciken da kasar Amurka ta kaddamar, tare da daukar matakai da suka dace domin kare ikonta yadda ya kamata. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link