Sin Ta Gina Tsarin Cajin Motoci Masu Amfani Da Lantarki Mafi Girma A Duniya
Kasar Sin ta gina tsarin cajin motoci masu amfani da lantarki mafi girma a duniya, wanda ka iya biyan bukatun motoci masu amfani da sabbin makamashi sama da miliyan 40.
Hukumar lura da makamashi ta kasar Sin NEA, ta bayyana a Larabar nan cewa, zuwa karshen shekarar 2025, jimillar cibiyoyin cajin motoci masu aiki da lantarki a kasar ya kai miliyan 20.092.
Hukumar NEA ta kara da cewa, na’urorin da ake bukata domin cajin motocin sun fafada matuka da gaske a shekarar ta 2025, inda karuwarsu cikin watanni 18 kacal ta kai miliyan 20 daga miliyan 10. (Mai fassara: Saminu Alhassan)