’Yan sa-kai sun hallaka ’yan bindiga 7 a Katsina
[ad_1]
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga bakwai sun mutu a wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen.
Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce jami’an tsaron al’umma na Community Watch Corps (CWC) sun yi artabu da maharan, inda suka daƙile harin.
A yayin arangamar, maharan sun ƙone motar jami’an tsaron, amma duk da haka, jami’an sun samu nasarar fatattakar su.
Danmusa, ya bayyana cewa, rahotanni sun nuna cewa wannan hari ramuwar gayya ne, bayan kashe wasu mahara a wani hari da suka kai Magajin Wando.
Ya yaba wa jami’an wajen kare al’umma, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro domin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
Haka kuma ya roƙi jama’a su ci gaba da bayar da rahoton motsin ’yan bindiga.
Hakazalika, ya jaddada cewa gwamnatin ci gaba da ƙoƙari wajen kare rayukan al’umma a jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link