Sanusi Mikail Sami ya zama sabon Sarkin Zuru

[ad_1]



Alhaji Sanusi Mikail Sami Gomo na III ya zama sabon Sarkin Zuru.

Kwamishinan Ƙananan hukumomi da masarautu, Alhaji Abubakar Garba Dutsin-Mari ne ya sanar da hakan yau Alhamis, a fadar Sarkin Zuru wanda kuma ya miƙa masa takardar naɗin da Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya sanya wa hannu.

Ya ce, naɗin sabon Sarkin ya biyo bayan miƙa sunayen sarakuna uku da  masarautar Zuru ta miƙa wa Gwamnan jihar, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya ƙara da cewa, Gwamnan wajen yin amfani da ikon da aka ba shi, ya amince da Alhaji Sanusi Mikail Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru, wanda yanzu aka amince da shi a matsayin Gomo III.

Tun da farko, Sarkin Wasagu, Alhaji Muktari Musa wanda ya riƙe muƙamin muƙaddashin Sarki tun bayan rasuwar marigayin, ya karɓi baƙoncin sabon Sarkin a hukumance tare da maraba da dukkan baƙi a fadar.

A nasa jawabin, sabon Sarkin ya nuna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da kuma Gwamna Nasir Idris bisa amincewar da aka yi masa.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da aminci da kuma haɗin kai, yana mai ba su tabbacin buɗaɗɗiyar manufarsu da kuma jagoranci na bai ɗaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *