’Yan bindiga sun sace likita da ɗan uwansa a Edo

[ad_1]



Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace mutum biyu ’yan uwan juna a garin Auchi, a Jihar Edo.

Waɗanda aka sace su ne Abu Ibrahim Babatunde da Abu Tahir.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a kan titin City Pride, Igbira Camp, Auchi, wanda shi ne hedikwatar Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma.

Abu Ibrahim likita ne da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jihar Edo.

Yana kan hanyarsa ta dawowa gida daga aiki tare da ɗan uwansa Tahir lokacin da aka kai musu hari.

Majiyoyi sun ce sun isa gidansu da misalin ƙarfe 7:30 na dare.

Yayin da Tahir ya fito daga mota domin buɗe ƙofa, sai ’yan bindigar suka fito ba zato ba tsammani.

Take suka yi garkuwa da ’yan uwan guda biyu, tare da yin awon gaba da su zuwa cikin daji.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin rundunar, Eno Ikoedem, ta ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 8:30 na dare a ranar 2 ga watan Janairu, 2026.

Ta ce an tura jami’an ’yan sanda zuwa yankin nan take.

Haka kuma, an fara bincike tare da haɗin gwiwar ’yan banga, masu gadin gandun daji da kuma sauran jami’an tsaro.

A cewarta, ana ci gaba da bincike a cikin dazukan yankin da ke kewaye, domin ceto waɗanda aka sace tare da kama masu laifin.

Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an ceto waɗanda aka sace.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *