Mace ta rasu a dakin saurayinta a Abuja
[ad_1]
Wata mata mai suna Esther ta rasu bayan ta ziyarci saurayinta a Abuja.
Lamarin, kamar yadda rahotanni suka nuna, ya faru ne a ranar Laraba a yankin Dei-Dei na Babban Birnin Tarayya.
Wani mazaunin yankin mai suna Dauda ya ce Esther ta bar gida a ranar Laraba don ziyartar saurayinta.
Ya ce daga baya saurayin ya kira babban ɗan uwanta da daddare ya sanar da shi mutuwar ta.
Dauda ya ƙara da cewa saurayin ya yi ikirarin cewa ya sayo mata abinci, bayan ta ci ta fara amai.
Ya bayyana cewa saurayin ya kai ta Asibitin Gwamnati na Kubwa, inda ta rasu yayin da ake ba ta magani.
Dauda ya ce saurayin ya kashe wayarsa da kuma ta Esther.
Ya ce, “Esther ta bar gida da rana a ranar 21 ga Janairu, 2026, ta sanar da ’yar uwarta cewa za ta je banki a Dei-Dei. Amma ba ta dawo gida ba.
“Daga baya da dare, a ranar, ɗan uwanta ya samu kiran waya daga wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin saurayin Esther. Mai kiran ya sake bayyana cewa Esther ta ziyarce shi a gidansa, inda ya sayo mata abinci. Bayan ta ci abincin, ta fara amai, hakan ya sa ya garzaya da ita Asibitin Gwamnati na Kubwa.
“Ya ce Esther ta rasu yayin da ake ba ta magani a asibitin. Tun daga lokacin lambar wayar saurayin ta kasance a kashe, haka ma ta Esther. Bai kuma bayar da sunansa ko adireshinsa ba.”
Da aka tuntubi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda a Babban Birnin Tarayya, Josephine Adeh, a ranar Juma’a, ta ce bincike na ci gaba da gudana.
Ta ce, “Mun san da lamarin kuma muna gudanar da bincike.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link