Lokaci Ya Yi Na Gyara Kura-kuran Da Aka Yi A Tarihi Tare Da Kin Amincewa Da Nuna Fin Karfi
[ad_1]
Kwanan nan, babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya zartas da daftarin kudurin da ya ayyana safara da bautar da mutanen Afrika bisa wariyar launin fata a matsayin mummunan laifi ga dan adam, bisa kuri’un nuna amincewa da kasashe 123 suka kada, tare da yin kira da a dauki matakan biyan diyya don gyara kura-kuran da aka tafka a tarihi. Kasar Ghana ce ta gabatar da daftarin kudurin a madadin rukunin nahiyar Afrika, kuma yadda aka zartas da kudurin ya shaida muhimmin ci gaba ga kasashe masu tasowa wajen tabbatar da adalci, wanda kuma ya kasance kyamar da al’ummu masu wayewar kai suka nuna ga laifukan mulkin mallaka da ma nuna fin karfi.
Cinikin bayi da aka yi ta tekun Atlantic babi ne mafi duhu a tarihin dan Adam. Daga karni na 16 zuwa na 19, an yi safarar miliyoyin mutanen Afirka, ciki har da mata da yara zuwa nahiyar Amurka ta tekun Atlantic, wadanda da yawa daga cikinsu sun mutu kafin isarsu, ragowar kuma an mai da su kayayyakin sayarwa tare da bautar da su. Cinikin bayi da aka shafe kimanin tsawon shekaru 400 ana yi ya lalata al’adu masu nasaba da siyasa na nahiyar Afirka, baya ga yadda ya gurgunta tsarin ci gaban tattalin arzikin nahiyar Amurka, wanda hakan ya haifar da manyan illoli ga nahiyar Afirka da ta Latin Amurka. Amma su kasashen yamma, ta hanyar cinikin bayi da bautar da su, sun samu ’yan kwadogo da kayayyakin sarrafawa da ma kasuwannin da suke bukata wajen raya masana’antu, kuma ta haka suka zama masu karfi da wadata.
Yadda MDD ta zartas da wannan kuduri abu ne mai matukar ma’ana, ganin yadda a karo na farko majalisar ta bayyana cinikin bayi a matsayin mummunan laifi ga dan Adam,wanda hakan ya tallafa wa kasashen Afirka ta fannin doka bisa bukatarsu ta neman a biya musu diyya, baya ga yin gargadi ga al’ummun duniya game da matsalolin nuna fin karfi da sabon salon mulkin mallaka da ake fuskanta a duniya.
Sai dai Amurka da Isra’ila da kuma Argentina sun kada kuri’ar rashin amincewa da kudurin, a yayin da wasu kasashen Turai da dama suka janye jikinsu daga kada kuri’ar, bisa dalilin wai “kasashen na yanzu bai kamata su dauki nauyin laifukan da suka aikata a tarihi ba” wadda ta zama hujja ga kasashen yamma da suka taba yin cinikin bayi ko mulkin mallaka a tarihi.
Amma ko wannan ya isa zama dalili?
A’a, sabo da na farko, kasashen yamma sun raya masana’antunsu ne bisa cinikin bayi, shi ya sa bai kamata su yi watsi da bukatar da kasashen da cinikin ya raunata ba. Na biyu kuwa, ko da yake a zamanin baya, babu dokoki da yarjejeniyoyin da suka haramta cinikin bayi, amma hakan ba ya nufin cinikin halal ne, musamman ta la’akari da ka’idar “ya kamata kasa ta dauki nauyin laifukan da ta aikata a duniya” da ake bi bisa dokokin kasa da kasa, bai kamata a ce kasar da ta aikata laifi ta daina daukar nauyin idan an samu sauyin mulki a cikin gidanta ko kuma idan wani laifi ne da aka aikata a lokacin baya ba. Har ila yau, in mun duba tarihi, Jamus ta taba biyan diyya ga Yahudawan da ’yan Nazi suka yi musu laifi a yakin duniya na biyu, kana Amurka ma ta biya diyya ga Amurkawa ’yan asalin Japan da ta yi musu daurin da bai dace ba a yayin yakin duniya na biyu, wato ke nan, kasashen yamma ba wai ba su san ya kamata a gyara idan an yi laifi ba, sai dai ba su so su gyara kawai.
Abin lura kuma shi ne Amurka ita kanta ta kafu ne bisa cinikin bayi da mulkin mallaka, wadda har yanzu ba ta kawar da wariyar launin fata daga tushe ba. Amurka ta biya diyya ga Amurkawa ’yan asalin Japan da ta yi musu daurin da bai dace ba a lokacin yakin duniya na biyu, amma kuma ta kaurace wa biyan diyya ga mutanen Afirka da ta yi wa laifi, hakan ya shaida yadda take nuna bambanci. Abin lura kuma shi ne, a yayin da Amurka ke musanta laifinta na mulkin mallaka, tana kuma dukufa a kan kafa sabon salon mulkin mallaka a sassan duniya,inda ta kama shugaban kasar Venezuala bisa matakan soja tare da neman kwatar albarkatun mai na kasar, kuma ta hada gwiwa da Isra’ila wajen kai hare-hare kan kasar Iran, matakin da ya lalata ikon mulkin kan kasar.
Lallai bai kamata a manta da tarihi ba, kuma ya zama dole a kyamaci ayyukan nuna fin karfi. Kasancewarta kasa mai tasowa da aka taba yi mata mulkin mallaka da hare-hare, kasar Sin ta san illolin mulkin mallaka da nuna fin karfi, don haka, kullum tana nuna cikakken goyon baya ga kasashen Afirka wajen neman a yi musu adalci, kuma za ta ci gaba da hada hannu da su, don fatan ganin an tabbatar da kudurin nan da MDD ta zartas, da kawar da tarnakin da aka yi wa nahiyar Afirka da tabbatar da farfadowarsu, tare kuma da kafa sabon tsarin duniya mai karin adalci.
[ad_2]
Source link