GORON JUMA’A 23-01-2026
[ad_1]
Jama’a barkabmu da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a, shafin da ke bawa kowa damar miƙa saƙon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziƙi, na kusa da na nesa, har ma da waɗanda aka daɗe ba a haɗu ba.
Kafin na fara da saƙonnin da kuka aiko mana, zan fara ga miƙa tawa gaisuwar zuwa ga; Fatima Musa Abubakar, da kuma Fatima Isah Aliyu, da Fatima Ya’u Ado, da Aisha, da kuma yayarta Nafisa Amarya, da kuma Maryama Abdull. Da fatan kuna tare da wannan shafi mai albarka na GORON JUMA’A, kuma da fatan za ku yi juma’a lafiya.
Yanzu kumƙ zan je ga saƙonnin da ku ka aiko mana kamar haka:
- An Kaddamar Da Aikin Samar Da Fitilu Kan Titi Masu Aiki Da Hasken Rana A Bujumbura Na Burundi Bisa Tallafin Sin
- Jerin ’Yan Wasan Da Za Taka Wa Super Eagles Leda A Gasar AFCON Ta 2026
Saƙo daga Safiya Idris, Jihar Kaduna:
Assalm. Ina so a miƙa min saƙona na gaisuwar juma’a zuwa ga ƙannena dake jihar Kano kamar su; Amira, Hadiza, Fauziyya, Salam, da Mubasshir. Sannan ina gaishe da Mamanmu maganin kukanmu Hajiya Habiba Idris, da haifinmu Alhaji Idris Munkaila. Ina fatan dukkaninsu saƙona zai je gare su.
Saƙo daga Fatima Buhari Muhd, Jihar Katsina:
Ina gaishe da mutanen Daura irin su; Iliyas Alkassim, Imman Halil, Zainab ‘yar baƙa, Muhammad Kareem, da kuma Deejo.da fatan za ku yi juma’a lafiya.
Saƙo daga Aliyu Ahmad Tijjani, Jihar Kano:
Dan Allah saƙon gaisuwata a miƙan ga Baffa Auwalu da kuma Leeti, da gwaggwa Maryama dake Birnin Kudu. Ina gaishe da Salisu mazan kwarai, ina gaishe ɗaya abokina Ahmad Ado, da ƙanwata shukura, da kuma iyayena ina gaishe su.
Saƙo daga Babban Yaya Minjibir:
Saƙona zan fara miƙawa ga iyalina gabaɗaya ‘ya’yana tun daga kana Uzaifa har zuwa Maimunatu, sannan ina gaishe da Mamata uwar ‘ya’yana Bilkisu. Ina yi wa al’ummar musulmi barka da juma’a ina fatan kowa zai yi sallar juma’a lafiya.
[ad_2]
Source link