An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da wani Hakimi da Dagaci a ƙaramar hukumar Funakaye bayan barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankinsu.
Rahotanni sun ce rikicin dai ya yi sanadin mutuwar ɗan sanda ɗaya tare da jikkatar wasu jami’an tsaro da dama.
Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Zubairu Muhammad, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kwamitin tsaro da aka gudanar ranar Laraba.
Ya ce an dauki matakin dakatarwar ne domin tabbatar da doka da oda, tare da aika sakon gargaɗi ga sauran masu rike da sarautun gargajiya cewa ba za a lamunci sakaci wajen dakile rikice-rikice ba.
“Majalisar ta yi nazari mai zurfi kan lamarin kuma ta nuna damuwa. Gwamnati ba za ta lamunci kai hari ga jami’an tsaro ko hana su gudanar da ayyukansu bisa doka ba. Duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji shi.
Barista Muhammad ya tabbatar da cewa an kama wasu da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa jami’an tsaron, kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamishinan ya ce kodayake ɗaya daga cikin shugabannin da aka dakatar ya rasa ɗansa a cikin lamarin, hakan bai hana gwamnati ɗaukar mataki ba saboda gazawarsa wajen hana rikicin ya ƙara kamari.
“Rahotanni game da halayen mamacin sun tayar da hankali. Da mahaifinsa, wanda shi ne shugaba a yankin, da ya ɗauki mataki tun da wuri, da ba a kai ga tashin hankali ba. Jagoranci na nufin jarumta da adalci,” in ji shi.
Kwamishinan ya sake jaddada goyon bayan gwamnati ga jami’an tsaro, inda ya yaba da jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya wanda ya sa jihar ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da suka fi kwanciyar hankali a ƙasar.
“Gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro don su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa. Duk wani yunƙurin tsoratar da su ko hana su aiki ba za a lamunce shi ba,” in ji shi.
Barista Muhammad ya kuma ambaci rahoton kwamiti ƙarƙashin tsohon Mataimakin Sufeton ’yan sanda na kasa, AIG Zubairu Muazu (mai ritaya), wanda ya binciki tushen rikicin na manoma da makiyaya a jihar.
Kwamishinan ya ce kwamitin ya gano toshe burtalolin kiwo na asali ta hanyar gonaki da gine-gine a matsayin babban abin da ke haddasa rikice-rikicen da ake ta fama da su.
Gwamnatin jihar ta kuma jaddada aniyarta ta kare zaman lafiya tare da yin gargaɗin cewa babu wanda za a rufa wa asiri idan aka same shi da laifin kawo barazana ga tsaro ko hana shari’a gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link