Dangote Da GCL Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Masana’antar Taki A Habasha
[ad_1]
Kamfanin Dangote da kamfanin makamashi na ƙasar China mai suna GCL Group sun ƙulla wata yarjejeniya ta shekaru 25 wadda kuɗinta ya kai dala biliyan 4.2 domin samar da iskar gas ga wani babban aikin masana’antar taki da za a gina a Ethiopia.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, kamfanin GCL zai riƙa samar da iskar gas ga sabuwar masana’antar urea mai ƙarfin samar da tan miliyan uku a duk shekara da Dangote ke shirin ginawa. Ana sa ran masana’antar wadda kuɗinta ya kai dala biliyan 2.5 za ta fara aiki a shekarar 2029, inda aka tsara mallakar kashi 60 ga Dangote da kuma kashi 40 ga Ethiopian Investment Holdings.
- Matatar Man Fetur Ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Da Dizal
- Matatar Dangote Ta Sake Ƙara Farashin Fetur Zuwa ₦1,175
Da zarar an kammala aikin, masana’antar za ta zama mafi girma a yankin Gabashin Afirka wajen samar da taki, inda za ta wadatar da buƙatar taki ta ƙasar Habasha tare da samar da shi ga ƙasashe maƙwabta.
Rahotanni sun ce za a samo iskar gas din ne daga filin gas na Calub Gas Field a yankin Ogaden, sannan a riƙa kai shi ta bututun mai mai tsawon kilomita 108 zuwa sabuwar masana’antar taki da za a gina a garin Gode.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce wannan haɗin gwuiwa zai taimaka wajen samar da tsarin haɗa masana’antar makamashi da samar da abinci a Afirka, tare da rage dogaro da shigo da taki daga ƙasashen waje.
[ad_2]
Source link