Gwamna Sule Ya Gabatar Da Kasafin ₦517.5bn Na 2026 Ga Majalisar Dokokin Nasarawa

[ad_1]


Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya miƙa kasafin kuɗin 2026 da ya kai darajar Naira biliyan 517.5 ga Majalisar Dokokin jihar, yana mai kiran shi “Kasafin Haɓaka Ci gaba”. A yayin gabatarwar da aka yi a Lafia, ya gode wa ’yan majalisar bisa yadda suke mara masa baya wajen tabbatar da ingantattun tsare-tsaren kuɗi. Ya ce kasafin ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta haɓaka masana’antu, karfafa manyan ayyuka da kuma ƙarfafa ci gaban tattalin arziki.

A cikin tsarin da ya gabatar, an ware N212.79bn (41.12%) don kashe-kashe na yau da kullum, yayin da N304.75bn za a karkatar zuwa manyan ayyukan raya kasa. Gwamnan ya ce irin wannan rabon ya nuna jajircewarsu wajen zuba jari a muhimman abubuwan more rayuwa da za su amfanar da jihar na dogon lokaci.

Bangaren tattalin arziki ya samu mafi yawan kaso da N221.84bn, sannan bangaren zamantakewa ya karɓi N170.92bn, yayin da gine-gine suka samu N157.80bn. Haka kuma ilimi ya karɓi N92.91bn, tsaro da gudanarwa N142.96bn, tare da bangarori kamar lafiya, noma, muhalli da yawon bude ido da suka samu rabonsu.

Da yake karɓar kundin kasafin, Kakakin Majalisar Dokoki, Dr. Danladi Jatau, ya tabbatar wa gwamna Sule cewa majalisar za ta yi aiki da sauri domin tabbatar da amincewa da kasafin. Ya jaddada bukatar ma’aikatu da hukumomi su kiyaye ka’idojin aiwatar da kasafi, ganin cewa bin tsari yana da tasiri wajen ingantacciyar gudanarwa. Ya kuma yaba da yadda gwamnati ke mayar da hankali kan ci gaban jama’a ta hanyar habaka fannonin da ke da tasiri kai tsaye a rayuwar al’umma.

Jatau ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da zaman lafiya da haɗin kai ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko kabila ba. Ya ce nasarar kasafin kuɗi da aiwatar da shi yadda ya kamata na bukatar fahimta da goyon bayan jama’a. A cewarsa, aikin raya Nasarawa abu ne da ya wajaba a dauka da muhimmanci domin tabbatar da dorewar ci gaba a dukkan kananan hukumomi.

Kakakin ya buƙaci al’umma su ci gaba da mara wa Gwamna Abdullahi Sule baya domin ganin an cimma burin da aka sa gaba na gina Nasarawa mai kwanciyar hankali da ci gaba. Ya ce majalisar za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa kasafin 2026 ya zama wata kafa ta kara wa jihar kuzarin tattalin arziki da walwalar jama’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *