Jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙone sansaninsu a Kogi

[ad_1]



Jami’an tsaro a Jihar Kogi, sun kama wasu ’yan bindiga biyu da suka ji rauni tare da likitocin bogi da ke yi musu magani.

Hakazalika, sun lalata sansaninsu a lokacin da suka kai musu farmaki.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Kogi, shawara kan harkar tsaro, Kwamanda Jerry Omodara (mai ritaya), ya bayyana cewa rundunar haɗin gwiwa da ta ƙunshi sojoji, mafarauta da ’yan sa-kai ne suka kai samamen a garin Aherin-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu.

A cewar Omodara, jami’an tsaron sun samu bayanan sirri cewa ana yi wa ’yan bindigar da suka ji rauni magani a wani gida.

Ya ce: “Mun samu bayanai cewa wasu ’yan bindiga biyu da suka ji rauni, ana musu magani a wani gida a Aherin-Bunu.

“Nan da nan muka tura jami’an tsaro, suka kama su tare da likitocin bogi da ke yi musu magani.

“Duk wanda aka kama yana taimaka wa ko yana haɗa kai da masu aikata laifi, za a hukunta shi ba tare da la’akari da muƙaminsa ba.”

Omodara, ya ƙara da cewa jami’an tsaron sun lalata sansanin ’yan bindigar, tare da ƙone wani wani waje da suke amfani da shi a matsayin asibiti da kuma gonakinsu.

Ya gargaɗi jama’a da su guji kowace irin alaƙa da masu laifi, inda ta jadadda cewa gwamnati ba za ta ƙyale duk mai tallafa wa miyagu ba a Jihar Kogi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *