Duk Da Barazanar Amurka, Iran Ta Jaddada Aniyarta Na Cigaba Da Tace Makamashin Nukiliya
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa, Tehran ba za ta taɓa yin watsi da tace makamashin Nukiliya (uranium) ba a tattaunawar da take yi da Washington, yana mai jaddada cewa, ba za su ji tsoron barazanar yaki da Amurka ba.
Ministan, ya shaida hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a Tehran wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya halarta, inda ya kara da cewa, Tehran ba ta da kwarin gwiwar amincewa da Washington.
“Za mu cigaba da tace sinadaran Uranium, duk da barazanar yaki, Domin babu wanda ke da ikon tsara mana rayuwarmu,” in ji Araghchi
“Jiragen yakinsu a yankin ba ya tsorata mu,” in ji shi, yana mai nuni da isowar wani jirgin ruwa mai dakon jiragen yakin sama na Amurka, USS Abraham Lincoln, a Tekun yankin na Arabiya.