Inshorar Lafiya A Matakin Farko Ta Sin Ta Karade Mutane Biliyan 1.33
Ya zuwa karshen shekarar 2025, sama da mutane biliyan 1.33 ne aka shigar da su cikin tsarin inshorar kiwon lafiya a matakin farko ta kasar Sin, yayin da adadin kason da aka karade ya kiyaye matsayinsa ba tare da tangarda ba da kusan kashi 95 cikin dari.
Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin ta ce, a shekarar 2025, asusun inshora na matakin farko, ciki har da inshorar haihuwa, ya samu makudan kudin shiga kimanin yuan triliyan 3.59, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 520, kana an kashe tiriliyan uku daga cikin asusun. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)