Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamfara
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta jaddada alkawarin kawo karshen matsalar Tsaro da ya ki ci yaki cinyewa a Jihar Zamfara da jihohin da ke fama da matsalar a arewa maso yamma da sauran jihohi.
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shatima ya bayyana haka a bikin ba da tutar Jam’iyyar APC ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal da ya gudana a Kasuwar Bajekoli da ke Gusau, babban birnin Jihar ranar Talata.
- ‘Yansanda Sun Ceto Mutane 7 Daga Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- CMG Ya Yi Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Lokacin Bazara” A Hadaddiyar Daular Larabawa
Sanata Kashin Shetima ya bayyana cewa, komawar Gwamna Dauda APC za a samu gagarimar nasara da ci gaban al’ummar Jihar Zamfara da kasa baki daya.
Kuma ya kawo hadin kan Jamiyyar APC a fadin Jihar ta Zamfara, domin yanzu haka, Jamiyyar PDP an yi jana’izar ta, ita kuma Jam’iyyar ADC bata da gurbi a Jihar ta Zamfara.
A nasa jawabin, gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da cewa, zai tafi da ‘yan Jam’iyyar baki daya babu wani banbanci a tsakanin ‘yar Jamiyyar.
Gwamna Dauda ya kuma dau alwashin ci gaba da ayyukan more rayuwa ga al’ummar Jihar Zamfara kamar yadda yake gabatarwa a yanzu haka.
A nasu jawaban, tsafin gwamnonin Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari da Ministan Tsaro, Bello Matawalle sun bayyana murnar su da godiya ga Allah da gwamna Dauda Lawal ya dawo cikin dangi.
Kuma sun tabbatar da cewa, babu wani dan takara a Shekara ta 2026 na gwamnan a Zamfara, sai gwamna Dauda Lawal
[ad_2]
Source link