Jawabin Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Na Taya Murnar Sabuwar Shekara Ta 2026

[ad_1]

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi na taya murnar sabuwar shekara ta 2026 a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2025, a birnin Beijing na kasar Sin, wanda ya kasance kamar haka:

Ya ku abokai maza da mata:

Barkanku da war haka! Shekara ta 2025 za ta wuce, sabuwar shekara ta 2026 tana daf da shigowa. A gabannin zuwan sabuwar shekara, ina muku fatan alheri daga nan birnin Beijing.

Shekarar bana ta 2025, shekara ce da aka kammala shirin raya kasa na kasar Sin, na shekaru biyar biyar na 14, wanda aka kaddamar da shi tun daga shekara ta 2021. A cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, duk da cewa, ana fuskantar matsaloli da kalubaloli iri daban daban, amma dukkan al’ummun Sinawa suna aiki tukuru, kuma sun cimma burin da aka tsara. A sa’i daya kuma, suna samun ci gaba kan sabuwar hanyar da suka kama, yayin kokarin zamanantar da kasa bisa salon kasar Sin. Kana GDPn kasar yana ta samun karuwa a cikin shekaru biyar a jere, inda aka yi hasashen cewa, adadin GDPn kasar Sin na shekarar bana zai kai kudin Sin Yuan triliyan 140. Ana iya cewa, karfin tattalin arziki, da karfin nazarin kimiyya, da na tsaron kasa, da hadadden karfin kasar Sin, dukkansu sun samu sabon ci gaba. Ban da haka, kasar Sin ta samu babban sakamako a bangaren kare muhalli, inda ake ganin ruwa mai tsabta da duwatsu masu dausayi ko ina a fadin kasar. Sakamakon haka, al’ummun Sinawa suna kara jin dadin rayuwarsu. Hakika ba abu ne mai sauki samun irin wannan sakamako a cikin wadannan shekaru biyar ba. Abu ne a fili, al’ummun Sinawa sun cimma burinsu na rayuwa cikin yanayi mai armashi ne ta hanyar hada hannu da yin kokari tare. Don haka, ina so in yi babbar godiya ga dukkanin ma’aikata, wadanda suka nuna kwazo da himma kan aikinsu.

A cikin shekara ta 2025, abubuwan da suka cancanci tunawa sun hada da shirya bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya, da kebe ranar tunawa da maido da yankin Taiwan daga mamayar kasar Japan. Nasarorin da ’yan mazan jiya a tarihin kasar suka samu sun karfafa wa al’ummun kasar gwiwa matuka, kuma ba za a manta da su ba har abada. Haka kuma ya dace a kara darajanta zaman lafiya, da ci gaba da yin kokari domin tabbatar da makomar kasa mai haske a nan gaba, yayin da ake kokarin farfado da al’ummun Sinawa.

Yanzu muna mai da hankali kan raya tattalin arziki mai inganci ta hanyar yin amfani da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, inda aka samu tarin sabbin sakamako bayan hada kimiyya da fasaha da masana’antu, musamman ma a bangaren kirkirarriyar basira ta fasahar AI. Kuma an samu sabon ci gaba wajen nazarin na’urar Chip bisa dogaro da kai, har ma kasar Sin ta kai sahun gaba a fannin daga matsayin kirkire-kirkire a fadin duniya. Misali, na’urar binciken sararin samaniya ta Tianwen-2 ta kaddamar da aikinta, an kuma fara gina babbar tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Yaxia, kana an kaddamar da babban jirgin ruwan tashi da saukar jiragen saman yaki mai majajjawar maganadisun lantarki irinsa na farko na kasar Sin. Ban da haka, mutum mutumin inji mai siffar dan Adam kirar kasar Sin sun fara nuna fasahar wasan Kung Fu, yayin da kananan na’urori masu tashi sama suka yi nune-nunen wasan wuta a kasar. Baya ga yadda kirkire-kirkiren kimiyya suka haifar da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, har ila yau sun ingiza kyautatuwar rayuwar al’ummun Sin bisa babban mataki.

Mun lura cewa, harkokin al’adu su ma suna kara habaka a kasar Sin, inda bukukuwan baje kolin kayayyakin al’adu da na tarihi suke kara samun karbuwa daga al’ummun kasar. Misali, siffofin zane mai motsi na fina-finan da aka nuna kamar su Wu Kong da Ne Zha suka shahara a fadin duniya. An lura cewa, al’adun gargajiya na kasar Sin suna kara jawo hankalin matasan kasar. An kuma ga alama cewa, kasuwar yawon shakatawan dake nasaba da al’adu ta kara habaka a kai a kai, inda aka shirya gasannin kwallon kafa ko kwallon raga a birane da kauyuka, ko shirya wasannin kankara a lokacin hunturu. Al’adun Sinawa suna kara samun ci gaba yayin da ake hada salon gargajiya da na zamani.

Ina son in ambaci wannan batu a nan, wato muna yin kokari tare domin jin dadin rayuwar kowa. Na taba zuwa jihar Xizang da ta Xinjiang domin halartar wasu bukukuwa. A lokacin, na ga al’ummun Sinawa, wadanda suke zama a kan duwatsun da kankara mai laushi ta rufe, ko a gefuna biyu na tsaunin Tianshan, dukkansu sun hada kai kafada da kafada domin nuna kaunarsu ga kasar Sin, da godiyarsu bisa rayuwarsu mai nishadi, ta hanyar mika kyautar farin kyalle ga manyan baki, da yin wake-wake da raye-raye. Kyautatuwar zaman rayuwar al’ummun kasar Sin shi ne kan gaba, don haka akwai bukatar a kula da shi a ko da yaushe. A cikin shekarar da ta shude, kwaskwarimar da aka yi kan aikin kyautata rayuwar tsofaffi ta amfanar da su sosai. Yanzu a duk wata, ana samar da tallafin kudi har Yuan 300 ga iyalan da suka haifi yara. Idan kowanne iyalin kasar Sin ya ji dadi, to, babban iyalin kasar Sin shi ma zai samu ci gaba yadda ya kamata.

Haka zalika, kasar Sin ta ci gaba da rumgume dukkan kasashen duniya. An shirya taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a birnin Tianjin, da taron kolin mata na duniya cikin nasara, kuma an kaddamar da tashar ruwa ta cinikayya maras shinge wadda ake samar da hidimomin harajin kwastam na musamman ta tsibirin Hainan. Domin dakile matsalar sauyin yanayi, kasar Sin ta sanar da wasu sabbin matakai. Baya ga shawarwarin raya kasa da kasa guda uku, na gabatar da shawarar inganta gudanar da harkokin kasashen duniya domin kafa tsari mai adalci a bangaren. Yanzu ana gudanar da manyan sauye-sauye a duniya, inda wasu yankuna suke fama da yake-yake. Har kullum kasar Sin tana nacewa manufar adalci, kuma tana son hada hannu da sauran kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a fadin duniya, tare kuma da gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya.

Kwanan baya, na halarci bikin bude gasar wasannin kasar Sin, inda na ga yadda lardin Guangdong, da yankunan musamman na Hong Kong da Macau suka yi hadin gwiwa yayin shirya gasar, wanda ya sa ni farin ciki kwarai. Nan gaba za mu ci gaba da nacewa manufar “Kasa daya, tsarin mulki iri biyu” domin samar da goyon baya ga yankunan biyu na Hong Kong da Macau, ta yadda za su kara taka rawar gani kan aikin raya kasar Sin, tare kuma da kiyaye wadata da kwanciyar hankali mai dorewa. Hakika akwai alaka ta jini tsakanin ’yan uwa na babban yankin kasar Sin da na yankin Taiwan, ko shakka babu za a cimma burin dunkulewar kasar Sin gaba daya, kuma babu wanda zai iya hana hakan.

Game da gina jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuwa, a ganina, idan an gina jam’iyyar yadda ya kamata, to, kasar Sin ita ma za ta kara samun karfi. Mun gudanar da horo ga ’yan jam’iyya kan ka’idojin da kwamitin kolin jam’iyyar ya tanada a bangarori takwas, kuma mun samu sakamako mai gamsarwa. Nan gaba kuma, za mu ci gaba da kokari domin neman cimma burin da aka tsara a birnin Yan’an na lardin Shaanxi, daya daga cikin wurare muhimmai ga jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

Shekara ta 2026, shekara ce da za a fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 15. Ya dace a ba da muhimmanci kan aikin, saboda mafarin aikin yana da nasaba da sakamakon da za a samu. Yanzu haka, ya dace mu cika da imani da kuzari domin ingiza bunkasar tattalin arziki mai inganci, da kara zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare daga dukkan fannoni, da kara samar da wadata ga al’ummun Sinawa, da kuma bude sabon babin kafa al’ajabin kasar Sin.

Duk wata matsalar da ka iya faruwa yayin neman cimma buri, idan mun yi matukar kokari tare, tabbas kokarinmu ba zai bi ruwa ba. Bari mu kara nuna kwazo da himma tare, kuma mu yi hobbasa, ta yadda za mu cimma muradun da muka tsara.

Yanzu ana dab da shiga ranar sabuwar shekara. Don haka ina yi wa kasarmu fatan kara samun kyautatuwa da wadata. Ina fatan kowa da kowa zai cimma burin da ya sanya gaba, a dukkan fannonin rayuwarsa. (Mai fassara: Jamila)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *