Peter Obi ya sauya sheƙa zuwa jami’yyar ADC a Enugu
[ad_1]
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, tare da wasu jiga-jigan ’yan siyasar yankin Kudu maso Gabas.
Sun sanar da wannan mataki ne a ranar Laraba a birnin Enugu bayan shafe watanni suna tattaunawa kan makomarsu a siyasa.
Shugabannin sun ce sun koma ADC ne domin samar da jam’iyyar adawa da za ta ƙalubalanci Tinubu da jam’iyyar APC.
Manyan ’yan siyasa da dama ne suka halarci taron, ciki har da Sanatoci, tsofaffin gwamnoni, da shugaban ADC na ƙasa, David Mark.
Hakazalika, wasu daga cikin shugabannin adawa daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun halarci taron.
Da yake jawabi a taron, Peter Obi ya ce wannan mataki alama ce ta fara sabuwar tafiya ta siyasa domin ceto Najeriya.
“Yau rana ce mai muhimmanci. Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, muna fata cewa a 2026 za mu fara tafiyar ceto Najeriya domin ci gaban tattalin arziƙi da haɗin kai,” in ji shi.
Obi ya kuma yi gargaɗi game da shirin aikata maguɗin zaɓe, inda ya yi kira ga hukumar zaɓe ta bi ƙa’idoji yadda ya kamata.
“Za mu yi tir da duk wani yunƙurin maguɗin zaɓe a 2027 ta kowace hanya ta doka da ta halatta,” in ji shi.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai a tsakanin jam’iyyun adawa, inda ya bayyan cewa Najeriya na buƙatar shugabanci na gari da zai magance matsaloli da rarrabuwar kai.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link