Peter Obi Da Shugabannin Kudu Maso Gabas Sun Koma Jam’iyyar ADC A Enugu
[ad_1]
Tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar ADC tare da wasu sanatoci da manyan ‘yan siyasa daga yankin Kudu maso Gabas.
Shugabannin sun sanar da wannan mataki ne a ranar Laraba a birnin Enugu, bayan shafe watanni suna tattaunawa.
- Dubu 100 Aka Biya Ni Na Sanya Bam A Masallaci A Borno — Ɗan Ƙunar Baƙin Wake
- Haraji: Gwamnati Ba Za Ta Cire Kuɗi Kai-Tsaye Daga Asusun Bankin Mutane Ba – Oyedele
Sun ce sun koma ADC ne domin samar da jam’iyyar adawa mai ƙarfi da za ta iya ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Manyan ‘yan siyasa da dama sun halarci taron, ciki har da sanatocin Kudu maso Gabas, tsofaffin gwamnoni, da shugaban ADC na ƙasa, David Mark.
Da yake jawabi a taron, Peter Obi ya ce wannan shawara alama ce ta fara sabon yunƙuri na ceto Nijeriya daga rashin kyakkyawan shugabanci.
Ya zargi gwamnatin APC da raunana dimokiraɗiyya, tare da alƙawarin haɗa kai da wasu domin samar da shugabanci na gari da haɗin kai a ƙasar.
[ad_2]
Source link