’Yan bindiga sun hallaka mutum 3, sun jikkata wasu a Nasarawa
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kunza da ke yankin Ashigye a Ƙaramar Hukumar Lafia, Jihar Nasarawa, inda suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama.
Harin ya auku a daren ranar Talata da misalin ƙarfe 10 na dare.
Mazauna yankin sun ce suna zargin harin na da alaƙa da rikicin da ke faruwa tsakanin makiyaya da al’ummar yankin.
Sun kuma ce lamarin ya biyo bayan wani hari da aka kai a baya, inda aka kai wa wasu Fulani biyu hari a kusa da yankin, aka kuma kashe ɗaya daga cikinsu.
Ƙabilar Migili da ke zaune a yankin ta tabbatar da faruwar harin tare da yin Allah-wadai da shi.
Shugaban Ƙungiyar Matasa ta Migili, Sheh Oli Christopher, ya bayyana harin a matsayin ta’addanci.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara tsaurara tsaro tare da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Sai dai Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Nasarawa, Bala Dabo, ya musanta zargin cewa makiyaya Fulani ne suka kai harin.
Ya ce babu wata hujja da ta danganta Fulani da lamarin, tare da kira ga hukumomin tsaro su gudanar da bincike.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta ce mutum uku sun rasu yayin da mutane tara suka jikkata.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da tura jami’an tsaro zuwa yankin.
Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da bayanin da zai taimaka wajen binciken lamarin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link