Gyaran Dokar Zabe: Yadda Jinkirin Majalisar Dattawa Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Zaben 2027
[ad_1]
Jinkirin majalisar dattawa wajen gyare-gyaren dokar zabe ta shekarar 2022, ya tsawaita lokacin shirye-shiryen hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na fitar da jaddawalin ayyukan zaben 2027, wanda hakan zai kawo tsaiko ga zaben.
A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, majalisar dattawa ta fuskanci suka kan jinkiri wajen gyaran dokar zabe ta shekarar 2022, wanda ka iya jefa zaben 2027 cikin rashin tabbas. An dai zargi majalisar dattawa da kawo jinkiri da gangan, wanda majalisar ta kare kanta a makon da ya gabata.
- Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
- Yadda Fasahar Sin Ke Agaza Wa Samun Wadataccen Hatsi A Afirka
A ranar Laraba da ta wuce, yayin da aka yi tsammanin majalisar dattawa za ta karbi rahoton kwamitin kula da harkokin zabe kan dokar gyaran zabe, sai zaman majalisar ya tsaya ba zato ba tsammani. Lokacin da aka kai ga yin la’akari da takardar shafi 238, wacce aka raba wa kowane dan majalisa, an daga zaman zuwa ranar Alhamis, sakamakon rashin halartar shugaban kwamitin, Sanata Simon Lalong.
“Za mu ba ‘yan majalisar dattawa damar komawa gida da rahoton su yi nazarin shi kuma idan muka dawo gobe, za mu yi wani zama na sirri na dan gajeren lokaci mu tattauna muhimman tanadi na dokar, sannan mu amince da ita,” in ji jagoran majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele.
Duk da haka, a ranar Alhamis, majalisar dattawa ta kasa daukar wani muhimmin mataki dangane da lamarin. Tattaunawar da Bamidele ya yi alkawari bai faru ba, yayin da ba a samu wani yunkurin amincewa da dokar ba. Haka zalika, wannan ba shi ne karo na farko da aka yi irin wannan alkawarin ba kuma aka kasa cika. A watan Oktoba na shekarar 2025, Bamidele ya ce majalisar dattawa na aiki cikin sauri don guje wa bata lokaci wajen sa hannu kan amincewa da dokar zabe kafin lokacin zabe.
“Daga yanzu (14 ga Oktoba, 2025) zuwa Disamba 2025, za mu tabbatar da kammala gyaran dokar zabe ta 2022 don ka da ta yi kusa da zaben 2027,” jagoran majalisar dattawa ya yi alkawari. Amma fiye da wata guda bayan karshen Disamba 2025, majalisar dattawa ta kasa amicewa da gyaran dokar zaben.
Sakamakon zaman na ranar Alhamis, masu ruwa da tsaki sun ci gaba da abin da aka saba gani. Majalisar dattawa tana jinkirta daukar mataki kan kudirin soke dokar zabe da gyara tun lokacin da majalisar wakilai ta amince da nata bangaren a ranar 23 ga Disamba, 2025, kafin su tafi hutu na Kirsimeti da sabuwar shekara.
A taron zaman majalisar dattawan na ranar Laraba, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya shaida wa abokan aikinsa da su nazarci rahoton kwamitin kafin yin la’akari na karshe a ranar Alhamis.
“Abokan aiki masu daraja, kamar yadda jagora ya shawarce mu, don Allah mu duba rahoton sosai kafin yanke shawara na karshe gobe,” in ji shi.
Sai dai kuma a ranar Alhamis ba a sami dubawa na karshe ba. Maimakon haka, majalisar dattawa ta shiga zaman sirri na awa uku wanda ya haifar da kafa wani kwamiti na daban, wanda a zahiri ya kara daga lokacin da ake zaton amincewa kudirin a watan Fabrairu, wanda kuma shi ne watan da ake sa ran INEC za ta fitar da sanarwar zaben 2027.
Tuni dai masu ruwa da tsaki suka nuna damu cewa majalisar dattawa na yin abin da bai kamata ba, sanarwar Akpabio na kafa kwamitin wucin gadi mai mambobi bakwai ya kara ta’azzara damuwarsu. An sanya wa kwamitin, wanda ake sa ran zai bayar da rahoto ranar Talata mai zuwa, kan aiki na gyara dokar zabe.
Shugaban kwamitin, Sanata Niyi Adegbonmire, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sahari’a, sauran mambobin kwamitin sun hada da Adamu Aliero, Aminu Tambuwal, Adams Oshiomhole, Danjuma Goje, Tony Nwoye, da Titus Zam.
Ana ana sa ran INEC za ta yi aiki da sabon dokar zabe don samar da ka’idoji na gudanar da zaben 2027, masu ruwa da tsaki na ci gaba da nuna damuwa kan takaitaccen lokaci yayin da majalisar dattawa ke jan kafa kan daukar mataki.
Sashe na 28(1) na dokar zabe ta 2022, ya umurci INEC da ta fitar da sanarwar zabe kasa da kwanaki 360 kafin ranar kada kuri’a. An yi zaben shugaban kasa na karshe a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, tare da tsammanin cewa zaben shugaban kasa na gaba zai gudana a watan Fabrairun 2027.
Amma akwai alamun da ke nuna cewa za a iya daga babban zaben, wanda ya jefa INEC cikin rudani wajen gudanar da shiri a karamin lokaci. Tsarin gyara da ke gaban majalisar dattawa na ba da shawarar a gudanar da zaben shugaban kasa da gwamna a watan Nuwamba 2026, wanda za a gudanar da shi kusan watanni hudu kafin yadda aka tsara.
Sashe na 4(7) na kudurin gyara dokar ya bayyana cewa, “Za a gudanar da zaben shugaban kasa da gwamnonin jihohi kasa da kwanaki 185 kafin karewar wa’adin mai rike da mukamin.” Ana sa ran wa’adin masu rike da mukamai a halin yanzu zai kare a ranar 29 ga Mayu, 2027.
Idan majalisar dattawa ta amince da wannan kudirin, INEC za ta fuskanci gajeren lokaci na kammala ayyukanta. Tare da kasancewar hukumar da aka sani tana dage zabe saboda rashin isasshen shiri ko da an ba ta fiye da kwanaki 300 don yin shiri, jinkirin majalisar dattawan yana ci gaba da zama mai lahani ga gudanar da zabukan da ke tafe.
Idan majalisar dattawa ta kasa amincewa da gyaran dokar zabe a wannan makon, lokacin zai takaita sosai. Duk wani canji da aka shigar a bangaren majalisar wakilai zai bukaci a daidaita ta hanyar kwamitin kafin a amince da shi, sannan a mika wa Shugaban kasa Bola Tinubu don sanya hannu.
Wannan kalubalen ta kashe kwarin gwiwa a tsakanin masu ruwa da tsaki kan zaben 2027, wanda zai kasance sahihin zabe fiye da na 2023, wanda aka sami matsaloli na zargin rashin daidaito. Wadannan matsaloli sun karu saboda gibin da ke cikin dokar zabe ta 2022, wadda ba ta tilasta matakan bayyana gaskiya kamar isar da sakamakon zabe ta na’ura, wani mataki da zai iya rage yin magudin zabe.
[ad_2]
Source link