Ba Za A Yarda Da Farfado Da Dabi’ar Japan Ta Amfani Da Karfin Soji Ba



A ranar 18 ga watan Nuwamba, jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin sun yi shawarwari da jami’an ma’aikatar harkokin wajen Japan a birnin Beijing. Bangaren kasar Sin ya sake gabatar da manyan korafe-korafe da rashin amincewa ga bangaren Japan bisa katobarar da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi.

A wurin kasar Sin, batun Taiwan “iyaka ce ta daban da aka shata jan layi”. Idan Takaichi Sanae ta dage kan tunzura kasar Sin kan wannan batu, babu wanda zai yi tsammanin irin mummunan sakamakon da zai haifar mata.

Bugu da kari, jerin kalamai masu tayar da hankali da abubuwan da Takaichi Sanae take aikatawa sun haifar da nuna adawa da suka masu yawa a lokaci guda daga kasashe makwabtan Japan. Hakan na nuni da cewa, kasar Japan ta zama babbar silar kawo cikas ga zaman lafiya a gabashin Asiya.

A matsayinta na babbar kasa da ke dora abubuwan da suka faru na tarihi a sikeli, matakin da kasar Sin ta dauka na mayar da martani ba wai kawai don ta kare ikon ‘yancin kai da martabar kasarta ba ne kawai, har ma da kiyaye zaman lafiya da kyakkyawan tsari da aka samu bayan yaki, da kwanciyar hankali na yanki, wanda ke zama ginshiki mai karfi wajen dakile sake farfadowa da dabi’ar Japan ta amfani da karfin soji. (Mai fassara: Yahuza)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *