Yadda Ake Zama Da Uwar Miji  (2)

[ad_1]

5)- Ki riƙa kwaɗaitar da mijinki a kan ya riƙa ziyartar su ko da kuwa a gari ɗaya suke.

Sannan ki riƙa kwaɗaitar da shi akan ɗaukan ki da ƴaƴanki ku je ku wuni mata, kin ga za ta ji daɗi, kuma ki kwaɓi ƴaƴanki kafin ku je, domin kada su yi ta mata dambe da rashin kunya da barna, su sa ta ji haushin ki ta ce baki ba ma jikokinta tarbiyya ba.

Sannan duk ƙawayen uwar mijinki ki riƙa girmama su suma, kuma ki riƙa musu kyauta daga lokaci zuwa lokaci, hikimar yin haka ita ce duk abin da ki ka ba su za su ba ta labari, kin ga za ta ji daɗi ta ƙara sonki.

Idan mijinki zai saya wa mahaifiyarsa zani, to kada ki yi mugunta, ke ki sa mai tsada ita kuma ki ce a saya mata mai araha wanda ba zai kai ko ina ba zai koɗe, idan ya saya miki mai kyau ita ma ki ce ya saya mata mai kyau.

  • Ɓata-gari Sun Kashe Matar Aure Da ’Ya’yanta 3 A Kano
  • Muhimmancin Koya Wa ‘Yan Mata Ayyukan Gida Kafin Shiga Gidan Miji

Ki riƙa tunatar da shi wurin saya musu kayan abinci, da yi musu sutura akai-akai, domin da ban tausayi ka ga namiji gidansa ana cin kaji amma miyar mahaifiyarsa kamar ruwan wanke kai. Wallahi sai Allah ya saka mata, idan ya sayo kaji goma ko bai ce ba, ki ce wane zan cire biyu in yi wa Inna miya mu je a kai mata, kuma shi ma zai ƙara sonki.

Sannan ko da wasa ka da ki sake ki riƙa zagin uwar mijinki, domin wallahi magana fa tana zagayawa, za ki yi mamakin jin maganganun banzan da kika yi ya kai kunnenta, babu ruwan ki, ko da ki na kyautata mata amma ba ta sonki ki ci gaba wata rana za ta soki, idan har kina kyautata mata.

Sannan idan kin je yi mata wuni, to fa kada ki zauna baki komai, ɗaki ya yi datti amma kin ƙi gyarawa, in ma son samu ne kina zuwa ki fara mata hidima, ki kwaso kayanta ki wanke, ki share ciki da wajen ɗakin, ki mata goge-goge, wata ma idan ta iya kitso har tsefe kan uwar mijinta take yi, ta wanke mata ta rangaɗa mata kitso, ko kuma ta ce a kira mai kitso ta biya kuɗin a yi mata.

Wannan duka muna ɗaukar su abin wasa, amma ba haka bane, rashin kula da su shi ya sa iyayen mazajenmu suke takura mana, suke tsanar mu, kuma wani lokacin suna da gaskiya, domin waɗansu suna daina zawa gaishe da iyayensu tun daga lokacin da suka yi aure, ke kuma baki iya kwaɗaitar da shi ba. Wannan shi zai saka ta fara cewa ke ce kike hana shi.

Waɗansu matan ma har zagin uwar miji suke yi duk inda kika zauna sai ka zagye ta, idan za ai mata zani mai tsada ki hana, baki zuwa gaishe ta, kin je mata wuni kina cika kina batsewa dole ta tsaneki. Suma ƴan’uwansa dole su tsane ki domin mahaifiyarsa ba ta sonki.

Ƴan uwa mata sai mu ɗauki darasi domin mu san irin dubarun da zamu zauna da uwar miji da kyau.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *