NAF Ta Yi Wa Maɓoyar ‘Yan Ta’adda Ruwan Bama-bamai A Dajin Sambisa, Ta Kashe Da Dama

[ad_1]


Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta tarwatsa wata sananniyar maɓoyar ‘yan ta’adda da ke Arra a cikin dajin Sambisa na jihar Borno.

An kai farmakin ne biyo bayan umarnin Babban hafsan sojin sama na Nijeriya (CAS) na yin dukkan abin da ya dace wajen kawar da duk barazanar ‘yan ta’adda bayan da suka yi wa sojoji kwanton ɓauna a jihar Borno.

Wata sanarwa da Kakakin Rundunar Sojin Sama, Air Cardre Ehimen Ejodame ya fitar, ta ce harin ya biyo bayan harin kwanton ɓauna da aka kai wa sojoji a ranar 17 ga Oktoba, 2025 a Jihar Borno inda aka kashe Birget Kwamanda da sojoji ciki har da ‘yan CJTF.

Ya ce, Rundunar Sojin Sama ta rundunar ‘Operation HADIN KAI’ bayan fara aiwatar da umarnin CAS, a ranar 19 ga Nuwamba, 2025, ta fara kai hare-hare bayan samun rahoton leken asiri (ISR) wanda ya tabbatar da zirga-zirgar ‘yan ta’addan a Kashomri.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *