Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC
[ad_1]
Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Yarima Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa, jam’iyyarsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP bai dawo kan mulki ba a babban zaben 2027.
A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ke yawo a Facebook, an ga Abbas yana jawabi ga magoya bayan APC a wani taro da ya yi da masu yada labaran jam’iyyar a karamar hukumar Gwale ta Jihar, inda ya yi wadannan kalamai.
“Koma meye zai biyo baya, Abba ba zai koma kan kujerar gwamna ba. Ko Kano ta zauna lafiya ko ta hautsine, babu ruwanmu, amma dole ne Abba ya sauka a kujerar gwamnan Kano,” in ji Abbas
[ad_2]
Source link