An Kammala Bita Ta Biyu Ta Liyafar Sabuwar Shekarar Doki Ta CMG
[ad_1]
A yau Lahadi ne babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya kammala bita ta biyu ta Liyafar Sabuwar Shekara ta 2026.
Baki dayan shirye-shiryen liyafar sun gudana daki-daki hade da juna ba tare da wata tangarda ba.
Yayin da sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar kasar Sin wato shekarar doki ta bana ke karatowa, tawagar masu bada umarni za ta ci gaba da gyara kowane shiri domin tabbatar da komai ya gudana yadda ya kamata. Ana sa ran a jajibirin shiga sabuwar shekarar, liyafar CMG za ta samar wa Sinawa da ke duk fadin duniya gami da abokanai ’yan kasashen waje damar murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta doki cikin farin-ciki da annashuwa. (FMM)
[ad_2]
Source link