Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuƙa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Quarters da ke cikin birnin Kano.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 9:30 na safe.

Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa, wanda ake zargin ya yi zazzafar taƙaddama da kakansa, Muhammad Dansokoto mai shekara 75 da kuma kakarsa, Hadiza Tasidi mai shekara 65, inda ake zargin ya kai musu farmaki da wuƙa, tare da jikkata su da dama.

An garzaya da dukkan waɗanda suka rasu zuwa asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu. Daga baya aka miƙa gawarsu ga ’yan uwa domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

SP Kiyawa ya bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mai yiwuwa wanda ake zargin ya sha kayan maye a lokacin da lamarin ya faru.

Ya kuma bayyana cewa, Kwamishinan ’yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin miƙa ƙarar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID), domin gudanar da bincike mai zurfi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *