Ana zargin mai shagon kemis da ya yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a Filato
[ad_1]
Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata.
Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da aka fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki.
Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama.
A cewarta: “A ranar Lahadin da ta gabata ce bayan ruwan sama ya fara sauka, sai kawai ya rufe ƙofar shagonsa ne kemis inda nake koyan sayar da magani.
“Ya yi barazanar zai kashe ni da almakashi, ya tube min kaya da ƙarfi, sannan ya tilasta min yin jima’i da shi.”
Wata babbar yayar budurwar wadda ke yawan zuwa rako ta gida idan ta tashi daga shagon sayar da magungunan, ta bayyana yadda ta tarar da ’yar uwarta a wani yanayi na daban bayan ta dawo gida da kanta.
Ta ce: “Ni nake zuwa na rako ta gida, amma ranar da ne je ban same ta ba, ashe mun yi sabanin hanya don ta riga ni komawa gida.
“Da misalin ƙarfe biyu muna kwance sai na ji tana kuka, sai na tambaye ta abin da ya faru, inda ta shaida min cewa Ibrahim ya yi mata fyaɗe.
“Da safe kuwa muka garzaya ofishin ‘yan sanda na C Division muka kai rahoto. Don haka babu abin da muke nema face a yi mata adalci.”
Duk da mai unguwar Gangare, Hassan Guda, ya tabbatar da lamarin, sai dai ya ce: “iyayenta ba su kawo rahoton kai tsaye wurina ba, sai dai na ji labari daga maƙwabci.
“A matsayina na shugaba, za mu tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi, an kuma gurfanar da shi a kotu. Muna kira ga jama’a su kwantar da hankali.”
Sai dai har yanzu wanda ake zargi yana gudunmawa, lamarin da ya sa jama’ar unguwar suka yi barazanar rufe unguwar baki ɗaya idan aka sake watsi da batun.
Haka kuma, ofishin ‘yan sanda na C Division dake Jos ya bai wa shugabannin unguwar awanni 24 su mika wanda ake zargi a hannunsu, in ba haka ba za a ɗauki mataki na doka.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link