Tinubu ya nada jami’in EFCC Daraktan Furfanarwa na Kasa
[ad_1]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Rotimi Oyedepo, SAN, daga hukumar EFCC a matsayin Daraktan Gurfanarwa a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.
Wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Disamba, wadda Omolabake Mafe ta sanya hannu a madadin shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Tarayya, ta tabbatar da cewa an yi wa Oyedepo sauyin wurin aiki daga Hukumar EFCC zuwa Ma’aikatar Tarayya ne bisa la’akari maslahar jama’a.
Sanarwa da Abiodun Oladunjoye, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Fadar Shugaban Ƙasa, ya fitar a ranar Talata, ta ce Oyedepo zai gaji Abubakar Babadoko, wanda zai yi ritaya a ranar 31 ga Disamba, 2025, bayan kammala shekaru takwas da doka ta tanada a matsayin daraktan gurfanarwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran Mista Oyedepo, wanda ya kammala karatun Lauya a Jami’ar Ilorin a shekarar 2007, sannan ya halarci Makarantar Lauya a 2008, zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen rage dogaro da lauyoyi na waje a manyan shari’o’i, tare da tabbatar da daidaito da tsari a dabarun shari’a na Gwamnatin Tarayya.
Kafin wannan naɗi, Oyedepo ya yi aiki a EFCC fiye da shekaru 15, inda ya ƙware wajen gurfanar da manyan laifukan tattalin arziki da kuɗi. Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban Sashen Bincike da Kula da Ayyuka.
Daga cikin shari’o’in da ya taka rawa, har da kasancewarsa memba na tawagar lauyoyin Gwamnatin Tarayya a shari’ar P&ID da Nijeriya.
An zaɓe shi a matsayin Ma’aikacin EFCC na Shekara a 2014, sannan aka karrama shi da lambar yabo ta Mafi Ƙwararren Lauyan Laifukan Kuɗi a 2019.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link