An Yi Taron Ayyukan Noma Na Kwamitin Tsakiyar Kasar Sin A Beijing

[ad_1]

An yi taron ayyukan noma na kwamitin tsakiyar kasar Sin a Beijing daga ranar 29 zuwa 30 ga Disamba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da muhimman umarnin kan yadda za a ci gaban ayyukan noma da kauye da manoma.

Ya nuna cewa, shekarar 2026 ita ce shekarar fara shirin bunkasa ci gaban kasar Sin da zamantakewar al’ummar na shekaru biyar-biyar karo na 15, kuma yin ayyukan noma da bunkasa kauyuka da manoma, suna da muhimmanci. Ya kamata a karfafa aikin zamanantar da kauyuka da ingzia farfadowar kauyuka a dukkannin fannoni, da gaggauta hadewar birane da kauyuka, ya kamata a ci gaba da samar da isashen hatsi, da inganta hada kyawawan filaye da kyawawan iri da kyawawan na’urori da kyawawan hanyoyi tare, don habaka yawan amfanin gona da ingancinsa. A kuma habaka cikakken iya gudanar da aikin noma da ingancin amfanin gona. Ya kamata a inganta tasirin manufofin karfafa aikin noma, da fa’idojin manoma da wadatar da manoma, don tabbatar da farashin abinci da sauran muhimman kayayyakin noma a matakin da ya dace, don kara kudaden shiga na manoma.

Kazalika, ya kamata a ci gaba da karfafa sakamakon kawar da talauci, a shigar da matakan tallafawa ayyukan yau da kullum cikin dabarun bunkasa kauyuka, a kuma yi kokarin hana komawa cikin talauci. Dadin dadawa, a ci gaba da inganta gina kauyuka masu dadin zama da gina kyawawan kauyuka bisa ga yanayin yanki. A kuma habaka matakin gudanar da harkokin kauyuka da gina al’adun samar da kyawawan kauyuka yadda ya kamata. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *