Sin Da Tanzania Sun Karrama Ma’aikatan Da Suka Rasu Yayin Gina Layin Dogo Na TAZARA
[ad_1]
Jami’an gwamnatocin Sin da Tanzania, sun karrama gomman ma’aikata Sinawa da suka rasa rayukansu, yayin ginin layin dogo na TAZARA, wanda ya hada kasashen Tanzania da Zambia, a gabar da ake bikin cikar layin dogon shekaru 50 da fara aiki.
A jiya Asabar, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun halarci makabartar birnin Dar es Salaam, inda aka binne gawawwakin Sinawan da suka sadaukar da rayukansu yayin ginin layin dogon, kana sun aza furanni kan kaburburan mamatan, a wani mataki na tunawa da gudummawarsu da kuma martaba su, albarkacin bikin sharar makabarta na “Qingming”, wato bikin gargajiya na al’ummar Sinawa da ake gudanarwa domin girmama mamata da tunawa da magabata.
Da yake tsokaci yayin ziyartar makabartar, ministan harkokin cikin gida na Tanzania Patrobas Katambi, ya jinjinawa layin dogon na TAZARA, yana mai bayyana shi a matsayin shaida ta zahiri ta hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kana wata alama dake nuni ga juriyar kawancen dake tsakanin Tanzania da Sin. Kazalika, Katambi ya jaddada bukatar kare kima, da zamanantar da layin dogon a matsayin wani bangare na ajandar farfado da shi.
A nata bangare kuwa, jakadiyar Sin a Tanzania Chen Mingjian, cewa ta yi sama da ma’aikata Sinawa 50,000 ne suka shiga aikin ginin layin dogon da aka gudanar cikin shekarun 1970, inda kuma 70 daga cikinsu suka rasu yayin gudanar da shi.
Bugu da kari, yayin bikin, babban manajan hukumar sufurin jiragen kasa ta Tanzania da Zambia Bruno Ching’andu, da mataimakin ministan harkokin wajen Tanzania da harkokin hadin gwiwar gabashin Afirka James Kinyasi Millya, sun gode wa kasar Sin, suna masu yabawa kawancen gargajiya dake wakana tsakanin kasashen biyu. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link