Yunkurin Kasar Amurka Na “Neman Cin Nasara” Ya Sa Sauran Kasashe Yin Watsi Da Ita
[ad_1]
A wani jawabin da ya yi ga majalissun dokokin kasar Amurka a kwanan baya, shugaba Donald Trump ya ce kasarsa na ta samun nasarori a duniya. Sai dai yunkurin kasar na “neman cin nasara” ya kan sanya mutanen duniya damuwa, da daukar matakai na yin watsi da kasar.
Misali, jaridar Business Day ta kasar Najeriya ta wallafa wata makala a shafinta na Intanet a kwanakin baya, wadda ta bayyana cewa, canzawar manufar harajin kwastam ta kasar Amurka ta sa ’yan kasuwar Najeriya damuwa, lamarin da ya sanya raguwar darajar kayayyakin da aka fitar da su daga Najeriya zuwa Amurka a shekarar 2025 da kimanin kaso 14%, bisa jimillar shekarar 2024. Baya ga haka, darajar kayayyakin da aka fitar da su daga Najeriya zuwa kasar Sin ta karu da kimanin 81% a cikin shekaru 3 da suka wuce. Kana ana sa ran ganin wani yanayi na gagauta karkata ga kasuwannin kasar Sin a cinikin da ’yan kasuwar Najeriya suke yi, bisa la’akari da manufar Sin ta yafe wa kasashe 53 dake nahiyar Afirka harajin kwastam, wadda za ta fara aiki a watan Mayun dake tafe.
A fannin hada-hadar kudi ma ana iya ganin yanayi na “karkata ga kasar Sin”. Misali, kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na kasar Amurka ya ruwaito Jeremy Awori, shugaban kamfanin Ecobank, na cewar manufar harajin kwastam ta kasar Amurka dake canzawa a kai a kai ta haifar da mummunan tasiri kan kamfanonin kasashen Afirka, saboda haka bangaren Afirka na kokarin rage dogaro kan dalar Amurka, maimakonta ana karkata ga kudin Sin RMB da kudaden kasashen Afirka wajen gudanar da ciniki.
Dalilin da ya sa ake samun wannan karkacewa shi ne, domin yadda aka gano bambanci. Misali, a kwanan nan, cibiyar nazarin tsare-tsaren duniya ta HORN ta kasar Kenya ta wallafa wani bayani a shafinta na Intanet, wanda ya kwatanta manufar kasar Sin ta yafewa kasashen Afirka harajin kwastam, da dokar samar da karuwar tattalin arziki da damammaki a Afirka (AGOA) ta kasar Amurka. Inda aka ce, bisa ka’idar AGOA, gwamnatin kasar Amurka za ta tantance damar kasashen Afirka na samun gatanci a kowace shekara, lamarin da ya haifar da yanayin rashin tabbas. Yayin da a nata bangare, manufar kasar Sin na da dorewa, kana ta kunshi ra’ayi kaucewa tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, saboda haka za ta ba kamfanonin kasashe daban daban damar zuba jari hankalinsu a kwance, ta yadda za ta haifar da gudunmowa ga yunkurin nahiyar Afirka na neman ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
To, ko da gangan kasar Sin ta yi wani abu don tabbatar da wannan yanayi na karkacewa? A’a. Kasar Sin ba ta yi komai ba, illa kokarin raya tattalin arzikinta, da ci gaba da zame wa kasashe daban daban abokiyar hulda da za su iya dogaro da ita, da neman samun nasarori tare da su. Hakika babbar manufar kasar ba ta taba canzawa ba. Ta haka, Sin tana kokarin samar da yanayi mai tabbaci ga duniya.
A nata bangare, kasar Amurka tana karbar karin harajin kwastam, duk da cewa ana takaddama a cikin gida kan wannan batu. Tana kuma neman wai “karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka”, yayin da take matsa musu lamba ta fakewa da batutuwan hakkin dan Adam, da addini. Kana duk da cewa tana takama wai tana “kiyaye zaman lafiya a duniya”, hakika tana kaddamar da yake-yake a duniya a kai a kai, ciki har da hare-haren da ita da Isra’ila suke kai wa kasar Iran a halin yanzu. Ko da yake tana haifar da tarin matsaloli a duniya, duk da haka kasar Amurka na tsammanin cewa tana samun nasarori. Ke nan tana neman “samun nasarori” ne bisa tushen haddasa damuwa, da hasara, da wahalhalu, da zubar da jinin mutanen sauran kasashe.
Ban san irin sakamakon da kasar Amurka za ta samu a karshe ba, amma na san tabbas sauran kasashe za su yi watsi da ita, don gujewa mummunan tasirin da take haifar wa duniya. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link