Jiragen yaƙin Amurka sun yi haɗari a Kuwait
[ad_1]
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu tarin jiragen yaƙin Amurka sun yi haɗari a Kuwait yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya rincaɓe.
Duk da yake ba ta bayyana musabbin haɗarin ba, amma sanarwar da Ma’aikatar Tsaron Kuwait ta fitar ta ce dukkanin fasinjan da ke cikin jirgin sun tsira da ransu.
Sanarwar wadda ba ta bayar da cikakkun alƙaluma kan adadin jiragen da haɗarin ya shafa ba, ta ce tuni aka kwashe fasinjan da ke cikin jiragen yaƙin waɗanda yanzu haka ke karɓar kulawa a asibiti.
Sai dai a gefe guda kuma ma’aikatar tsaron ta ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin haɗarin.
Kafin sanarwar ma’aikatar tsaron ta Kuwait, wasu bidiyo a shafukan sada zumunta ne suka nuna wani jirgin yaƙin Amurka na ci da wuta a sararin samaniya gab da sansanin Sojin Amurka.
Tuni dai Iran ta yi iƙirarin kakkaɓo jirgin kodayake ita ma ba ta bayar da bayani kan sauran jiragen da suka yi haɗarin ba.
Zuwa yanzu Sojin Amurka 3 ne suka mutu a hare-haren Iran yayin da wasu 5 suka jikkata waɗanda Donald Trump ya sha alwashin ɗaukar fansar su.
Ana dai fargabar cewa akwai yiwuwar salwantar rayukan ɗimbin Sojin Amurka tare da jikkatar wasu gabanin kawo ƙarshen wannan yaƙi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link