Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a Gaza, Mohammed Sinwar

[ad_1]



Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza.

Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama.

Hotunan da Hamas ta fitar ranar Asabar sun nuna Sinwar tare da wasu manyan shugabannin siyasa da na soji, waɗanda aka bayyana a matsayin “shahidan kwamitin soji.”

Mohammed Sinwar, shi ne ƙanen Yahya Sinwar wanda Isra’ila ke zargi da jagorantar harin ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra’ila, rikicin da har yanzu wutarsa ke ƙara ruruwa.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa Mohammed Sinwar ya jagoranci kwamitin sojin Al-Qassam Brigades bayan mutuwar kwamanda Mohammed Deif.

Tun dai a ranar 13 ga watan Mayun da ya gabata ne rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe Mohammed Sinwar, wanda a watan Yuni kuma aka gano gawarsa a wani rami ƙarƙashin Asibitin Turai da ke Khan Yunis.

A watan Oktoban 2023 ne Hamas ta ƙaddamar da hari a Kudancin Isra’ila, inda sama da mutum 1,219 suka mutu.

Hakanan daga cikin mutum 251 da Hamas ta yi garkuwa, rahotanni na nuna cewa akwai aƙalla mutum 47 da har yanzu take tsare da su a Gaza, ciki har da kusan 20 da ake ganin suna raye.

Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ta tabbatar da sahihancin alƙaluman, ta ce martanin da Isra’ila ta mayar ya jawo asarar rayuka masu yawa a Gaza, inda ma’aikatar lafiya ta Gazan ta ce sama da mutane 63,371 — mafi yawansu fararen hula — sun mutu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *