Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu
[ad_1]
Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Tun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar.
Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba ta ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas ba kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na watan Satumba.
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, Starmer zai yi jawabi ga al’umma kan matsayarsa, gabanin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya, inda ƙasashe 10 ciki har da Faransa za su amince da kafa ƙasar ta Falasɗinu.
Sai dai Amurka da Isra’ila sun soki matakin, suna bayyana shi a matsayin saka wa Hamas duk da harin da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Su ma ƙasashen Portugal da Canada da Australia sun ce za su amince da ƙasar Falasɗinun a cikin wannan mako.
Daga gobe Litinin ce sama da shugabannin ƙasashe 140 ne za su hallara a birnin New York domin taron shekara-shekara na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Matsalar jinƙai da ta addabi yankin Falasɗinu za ta kasance a kan gaba a tattaunawar da za ta gudana a taron na bana.
Shugaba guda da ba zai halarci taron a zahiri ba shi ne shugaban Falasɗinawa, Mahmud Abbas, wanda Amurka ta hana biza tare da waɗansu jami’ansa.
A karo na musamman, babban zauren ya kaɗa ƙuri’a a ranar Juma’a domin bai wa Abbas damar gabatar da jawabi ta hanyar bidiyo, yayin da jakadan Falasɗinu zai wakilce shi a cikin ɗakin taron.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link