IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka
[ad_1]
Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka.
Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta.
A cewar sabon ƙudurin da ƙasashe 19 suka yi na’am da shi, dole Tehran ta bayar da kai bori ya hau ta hanyar sallama duk wasu bayanai gamsassu, da kuma ba wa ƙwararrun jami’an IAEA damar shiga wuraren da take gudanar da shirinta na bunƙasa makamashi.
Ƙudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da damar ziyartar tashoshinta na nukilya, ciki har da waɗanda aka kai wa hari lokacin yaƙi tsakaninta da Isra’ila a watan Yuni.
Ƙasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Amurka ne suka bijoro da ƙudurin wanda Rasha da China da kuma Jamhuriyyar Nijar suka hau kujerar naƙi wajen kaɗa ƙuri’a.
China da Rasha dai sun nuna fargaba kan abubuwan da ka iya biyowa baya, idan aka samar da sabon ƙudurin, wanda suka ce ka iya sa Iran ta bijire wa batun, duba da takun saƙar da aka fuskanta a baya-bayan nan a tsakanin jami’an hukumar IAEA da fadar mulki ta Tehran.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link