Amurka ce za ta riƙa ba da umarnin duk wani mataki da Venezuela za ta ɗauka — White House

[ad_1]



Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta kasance mai rinjayen iko kan dukkan matakan da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Venezuela za ta ɗauka, bayan kama tsohon shugaban ƙasar, Nicolas Maduro.

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce Amurka na da “cikakken iko da tasiri” a halin yanzu kan shugabancin riƙon ƙwarya na Venezuela, inda ta ƙara da cewa duk wasu muhimman shawarwarinsu za su riƙa fitowa ne bisa umarnin Amurka.

Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, tana mai cewa Shugaba Donald Trump zai gana da shugabannin kamfanonin mai na Amurka a ranar Juma’a domin tattauna makomar harkar man fetur ta Venezuela.

Trump ya sha nanata cewa Amurka za ta riƙa tafiyar da harkokin Venezuela, duk da cewa babu sojojin Amurka a ƙasar.

Rahotanni na nuna cewa Washington na amfani da takunkuman hana fitar da man Venezuela ta teku da kuma barazanar ƙarin matakan soja domin tilasta haɗin kai daga shugabar riƙon ƙwarya, Delcy Rodriguez.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce gwamnati na da cikakken tsari kan yadda za ta tafiyar da al’amuran Venezuela, bayan wasu ‘yan majalisa sun nuna shakku.

Trump ya ce Venezuela za ta miƙa ganguna miliyan 30 zuwa 50 na man fetur ga Amurka, yayin da kamfanonin mai na Amurka za su zuba jari a cibiyoyin man ƙasar, kodayake har yanzu babu kamfanin da ya tabbatar da hakan.

A gefe guda, Amurka ta ƙara tsaurara matakanta ta hanyar ƙwace wani jirgin dakon mai a Tekun Atlantika, tana mai cewa jirgin na safarar man da aka ƙaƙaba wa takunkumi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *