Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci

[ad_1]



’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16.

An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa.

Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar.

Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford, ya ƙaryata ikirarin nata.

Ya ce: “Duk da cewa shekaru 30 sun shuɗe, amma tabbas da zan tunawa idan da mun taɓa ɗaukar wata ɗalibar Najeriya bisa wani tallafi — gaskiya ba mu yi ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami’ar ba ta ɗaukar ɗalibai bisa sakamakon SAT kaɗai, kuma ba ta bayar da tallafin ragin kuɗi ba; domin idan ɗalibi na bukatar $30,000 a shekara, ragi ba shi da amfani domin ba zai iya wucewa ba.

Haka kuma, ya ce bai taɓa samun umarnin sauke shawarar sa ba daga wani shugaba a jami’ar.

Masu suka daga cikin jam’iyyun Labour da Liberal Democrats sun buƙaci Badenoch da ta bayyana dalilin wannan iƙirarin, saboda haƙƙin jama’a ne su san gaskiya, musamman abin da ya shafi shugabar adawa.

Duk da wannan tirjiyar, Badenoch ta tsaya kan cewa ta samu tayin bisa ga sakamakon SAT ɗinta.

Ta ce: “Na tuna ranar da wasiƙun suka iso a gare ni — ba na da takardu yanzu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *