Ƙasashen Musulmi sun soki Isra’ila kan rufe Masallacin Al-Aqsa a Ramadan
[ad_1]
Ƙasashen Larabawa da na Musulmi guda takwas sun yi tir da Isra’ila ranar Alhamis kan ci gaba da rufe Masallacin Al-Aqsa da ke Kudus a daidai lokacin azumin watan Ramadana mai alfarma.
Isra’ila ta rufe dukkan wurare masu tsarki a tsohon birnin Kudus na Gabas saboda dalilai na tsaro, bayan da ta ƙaddamar da hare-haren sama tare da haɗin gwiwar Amurka kan ƙasar Iran, lamarin da ya haddasa yaƙin yankin baki ɗaya.
Wannan rufewar ta zo ne daidai da lokacin Ramadana, lokacin da dubun-dubatar Musulmin Falasɗinu suka saba yin sallar Juma’a a masallacin — wanda shi ne wuri na uku mafi tsarki a Musulunci.
Ministocin harkokin wajen ƙasashen Pakistan da Masar da Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Indonesia da Turkiyya da Saudi Arabiya da ƙatar sun bayyana cewa ci gaba da taƙaita zirga-zirgar “ya saɓawa doka kuma ba shi da hujja”, sannan kuma tsokana ce” ga masu ibada.
A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, sun ce hakan, “keta dokokin ƙasa da ƙasa ne a fili… da kuma ƙa’idar ba da damar shiga wuraren ibada ba tare da hani ba”.
Rundunar ‘yan sanda ta sanar a ranar Litinin cewa, dukkan wurare masu tsarki a tsohon birnin, ciki har da katangar Western Wall, Masallacin Al-Aqsa, da wurin bauta na Temple Mount, (wanda Musulmai ke kira Haram al-Sharif) wuri ne mai tsarki da ake takaddama a kai a Kudus da Cocin Holy Sepulchre, za su ci gaba da kasancewa a rufe domin “kare lafiyar jama’a da rayukan mutane”.
Isra’ila ta mamaye gabashin Kudus ne a shekarar 1967, sannan daga baya ta haɗe shi da ƙasarta, matakin da ƙasashen duniya ba su amince da shi ba.
Tun farkon fara yaƙin, hukumomin Isra’ila sun hana kowa shiga tsohon birnin saboda dalilai na tsaro, in ban da mazauna wurin ko masu shaguna.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link