Ba mu da hurumin shiga yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran — Jamus

[ad_1]



Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta shiga yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran ba.

Merz ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Berlin a ranar Litinin.

Shugaban ya ce ba su da wani dalili na shiga yaƙin saboda tun farko ya bayyana cewa yaƙin ba na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ba ne.

Ya ƙara da cewa Amurka da Isra’ila ba su tuntuɓe su ba kafin fara wannan yaƙi saboda haka babu yadda Jamus za ta shiga wannan ta kowace fuska.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *