Ambaliya ta kashe mutum 108 iyalai 2,700 sun rasa muhallansu a Kenya
[ad_1]
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 108, tare da raba iyalai sama da 2,700 da matsugunansu a sassa daban-daban na ƙasar Kenya.
Mutane 108 sun rasa rayukansu, yayin da sama da iyalai 2,700 suka tsere daga gidajensu sakamakon ruwan sama mai yawa da ambaliya a Kenya.
Hukumar ’Yan Sanda ta ƙasar ce ta bayyana alkaluman, bayan makonni da dama da ake fama da ruwan sama da ambaliya a sassan ƙasar.
Ambaliyar gaggawa da ta fara a daren 6 ga Maris ta yi mummunan ɓarna a faɗin ƙasar, inda ta tafi da motoci da dama, ta katse zirga-zirgar jiragen sama, tare da lalata layukan wutar lantarki.
Ko da yake ruwan sama ya ragu a wasu yankuna, ’yan sanda sun gargadi jama’a cewa haɗarin ambaliya na ci gaba, saboda toshewar magudanan ruwa da ƙasar da ta jiƙe.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link