Babu ƙasar da za ta tsoma mana baki wajen naɗa sabon jagora — Iran

[ad_1]



Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya yi Allah-wadai da abin da ya kira tsoma bakin Amurka cikin harkokin cikin gidan Iran.

Iravani ya mayar da martani ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana son taka rawa wajen zaɓen wanda zai gaji jagoran addinin Iran Ali Khamenei, wanda aka kashe a farkon rikicin da ake yi.

Da yake zantawa da manema labarai a New York, Iravani ya ce kalaman Trump sun saɓa da ƙa’idar rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashe kamar yadda kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya ya tanada.

Ya ce: “Iran ƙasa ce mai cikakken ‘yanci da cin gashin kanta. Ba ta amince kuma ba za ta taɓa yarda wata ƙasa ta tsoma baki cikin al’amuranta na cikin gida ba.”

Jakadan ya ƙara da cewa zaɓen sabon shugabancin Iran zai gudana ne bisa tsarin kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma muradin al’ummar Iran kaɗai, ba tare da wani tasiri daga waje ba.

A wata hira da kafar labarai ta Axios, Trump ya ce yana ganin ya kamata ya kasance cikin waɗanda za su taka rawa wajen naɗa sabon jagoran Iran.

Ya kuma ce bai ɗauki ɗan marigayi Khamenei a matsayin wanda ya dace ya gaje shi ba.

A nasa ɓangaren, Iravani ya sake jaddada cewa matakin da Iran ta ɗauka na mayar da martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila ya kasance halastacce kuma daidai gwargwado.

Ya kuma ce ana ci gaba da bincike kan zargin kai hare-hare kan wuraren da ba na soji ba, yana mai cewa wasu daga cikin hare-haren na iya zama sakamakon katsalandan ko karkatar da makaman da tsarin kariyar Amurka ya yi daga inda aka nufa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *