Rashin Tsaro Yayi Sauƙi A Mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu – Daniel Bwala
[ad_1]
Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Huldar Manufofin gwamnati, Daniel Bwala, ya ce matsalar rashin tsaro a Nijeriya bai kara ta’azzara ba, inda ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya na ɗaukar matakai na dindindin don rage tasirin matsalar.
Bwala ya bayyana hakan ne a shirin Head to Head na Al Jazeera, da Mehdi Hasan ke gabatarwa a Conway Hall, wanda aka wallafa ranar Juma’a ta kafafen sada zumunta na shirin. Ya amince cewa rashin tsaro yana nan, amma ya ce ba a samu taɓarɓarewar yanayi ba a ƙarƙashin gwamnatin yanzu. Ya kuma bayyana cewa babu ƙasar da ke cikakken tsaro, inda ya kawo wasu sassan London a matsayin misali.
- Yaƙin Iran: Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Matakan Tsaro A Yankin Gabas
- Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
Bwala ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na aiki tare da ƙasashen duniya wajen yaƙi da ta’addanci, inda ya ambaci tafiyar Shugaba Bola Tinubu zuwa Turkey da haɗin gwuiwa da Amurka, tare da sanar da cewa an kama shugabannin Boko Haram da Lakurawa watanni shida kafin maganganun Donald Trump. Game da ƙaruwar satar mutane, ya bayyana hakan da matsalar a matsayin “tattalin arziƙin” amma ya tabbatar da cewa gwamnati na ɗaukar matakai don magance ta.
Ya kuma bayyana cewa shirin Safe Schools Initiative yana taimakawa wajen kwashe ɗalibai daga wuraren da rashin tsaro ya fi yawa zuwa biranen jihar masu tsaro, don tabbatar da samun damar karatu lafiya.
[ad_2]
Source link