Iran ta nemi afuwar maƙwabtan ƙasashe ta gindaya sharaɗin daina kai musu hari
[ad_1]
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya ce sun dakatar da kai hari ƙasashen da ke maƙwabtaka da su bisa sharaɗin Amurka ba za ta yi amfani da ƙasashen wajen kai masu hari ba.
Wannan na cikin wani jawabi da kafafen yaɗa labarai na Iran suka wallafa a ranar Asabar, inda kuma shugaban ya bayar da haƙuri ga ƙasashen kan hare-haren da suka faru a kwanakin baya tun bayan fara yaƙi tsakanin ƙasar da Amurka da kuma Isra’ila.
A cikin wani saƙon bidiyo da aka yaɗa ta gidan talbijin na ƙasar, Mista Pezeshkian ya ce “ya zama wajibi mu nemi wannan afuwa na ƙasashen da muka kai wa hari.
“Ba mu da niyyar far wa maƙawambtanmu.”
Pezeshkian ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar ta bai wa sojojin ƙasar umarnin “daga yanzu kada a sake kai wa wata ƙasa maƙwabciyarmu hari, in ba ita ta fara kawo mana harin ba.
“Ga waɗanda ke tunanin za su yi amfani da wannan lokaci da muke ciki don kai wa Iran hari, su sani ba za mu ƙyale ba, kuma goyon bayan Isra’ila ko Amurka ba hanya ce ta girmama ’yanci ba,” in ji shi.
Tun dai bayan da Isra’ila da Amurka suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran tare da kashe jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link