Limamin da ya taɓa ba Kiristoci 262 kariya lokacin rikicin Filato ya rasu

[ad_1]



Abubakar Abdullahi, Limamin kauyen Nghar a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato, wanda ya ba Kiristoci 262 mafaka a masallaci yayin wani rikicin addini a yankin ya rasu.

Saleh Abubakar, ɗan Limamin, ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa ga Aminiya a ranar Juma’a, inda ya ce ya rasu da daren Alhamis a Asibitin Ƙwararru na Filato da ke Jos.

A cewar ɗan mamacin, mahaifinsa “ya rasu kwanaki 10 bayan an kwantar da shi a asibiti. An fara gano yana da matsalar zuciya. Yakan je a duba lafiyarsa ya dawo. Tun bayan gano cutar lafiyarsa ta shiga matsanancin yanayi.”

Limam Abubakar, makiyayi, ya rasu yana da shekara 90, ya bar ’ya’ya 19 ciki har da maza 12 da mata 7.

A watan Yuni 2018, lokacin rikicin addini mai tsanani da ya shafi kauyuka 10 a Barkin Ladi, marigayin ya ɓoye Kiristoci 262 a cikin masallaci da gidansa har sai da rikicin ya ƙare, inda ya ceci rayukansu daga hallakawa.

Ya samu lambobin yabo da dama saboda jarumtarsa, ciki har da lambar yabo ta ’Yancin Yin Addini ta Ƙasa da Ƙasa wacce Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba shi a shekarar 2019.

Kazalika, ya taɓa lashe lambar yabo ta fitattun mutanen da suka hidimta wa al’umma.

Za a binne marigayin yau bayan Sallar Juma’a a kauyen na Nghar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *